
Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta koma matakinta na farko a teburin La Liga, bayan da ta doke Borussia Dortmund 4-2 ranar Asabar.
Wasan farko da tsohon kociyan Chelsea, Thomas Tuchel ya ja ragama bayan da ya maye gurbin Julian Nagelsmann, wanda ta sallama.
Minti 13 da fara wasa Dortmund ta ci gida ta hannun Gregor Kobel daga nan Bayern ta kara uku ta hannun Thomas Mueller da ya ci biyu da kuma Kingsley Coman.
Daga baya Dortmund ta zare biyu ta hannun Emre Can a bugun fenariti da kuma wadda Donyell Malen ya ci daf da za a tashi.
Tun a minti na 23 Bayern ta ci 3-0, ba wani kocin kungiyar da ya ci kwallaye haka da sauri a tarihin kungiyar.
Wasa na 53 kenan a gida a Bundesliga da Bayern kan zura kwalo a raga a jere a kalla koda daya ne.
Rabon da Bayern ba ta ci kwallo ba a gida tun 0-0 da ta tashi da Leipzig a Fabrairun 2020.
Bayern tana matakin farko a teburi, bayan wasa 26, wadda wadda ke wannan matakin kan lashe Bundesliga a kaka 15 baya a gasar.
Wadda ta kasa dauka bayan tana matakin farko a wasa 26 ita ce Schalke a 2006/07, inda abokiyar hamayya Stuttgart ta lashe kofin.
Bayern Munich ba ta taba rashin nasara ba idan har Coman ya ci mata kwallo a wasa, wadda ta yi nasara 31 da canjaras daya.
Chelsea ta kori Tuchel a farko farkon fara kakar bana, yanzu kungiyar ta fada rashin kokari a gasar Premier League.
Kungiyar Stamford Bridge za ta kece raini da Real Madrid a wasan quarter finals a Champions League gida da waje a watan nan.