Tumatir ya fara araha a Kudancin Najeriya


Farashin tumatir da ke zaman daya daga cikin sinadaran hada miya kana mai matikar muhimmanci a rayuwa ya tashi a watannin baya, sai dai yanzu farashin ya sauko kasa warwas.

 

Kasuwar tumatir a jihar Rivers da ke Najeriya

 

A Kudancin Najeriya inda ake safarar tumatir daga Arewacin kasar, sai da kwando tumatir ya kai kusan naira 20,00, musamman a Fatakwal babban birnin jihar Rivers. To ganin yadda yanzu farashin na tumatir ya fado da kaso kusan sama da 50 cikin dari yasa A24N tai tattaki zuwa kasuwar sauke Tumatir din da ke Fruit Garden a D Line, a Fatakwal din. Shugaban kasuwannin jihar Rivers kana shugaba na musamman a kasuwar ta tumatir Chief Maxwell Nwala wanda ya ce:

Sayo tumatir daga kasashe makwabta

Akwai karancin tumatir a watannin Mayu da Yuni da suka wuce, inda ya tilasta muka ringa sayo tumatir din daga Kamaru, hakan kuma yasa farashinsa ya tsananta inda ake sayan karamin kwando naira 14,000. Haka dai muka shiga yin addu’o’i kan wannan bala’i na rashin tumatir a Najeriya, yanzu gashi mun fara samun tumatir daga Benue da Jos ga kuma na Zariya ya fara zuwa. Farashinsa yanzu ya yi wo kasa daga naira 14,000-15,000 ya zuwa naira 5,000 kacal.”

Wata Mata Madam Anne Nwode da ke sayar da tumatir din a wannan kasuwa kuwa cewa take:

“Farshin kwandon tumatir a baya ya kai naira 21,000-25,000, amma yanzu tumatir ya samu kwarai kuma farashin ya yi kasa sosai domin cikin roba karama ta fenti yanzu naira 1000 ne ko kuma 800, wanda a baya har naira 3,500 ake sayarwa.”

Matsalar tsutsa da ruwan sama mai yawa

Kwararru kan harkokin gona dai sun tabbatar da cewar karancin na tumatir da aka samu a baya ya faru ne a sakamakon matsalar tsutsa mai suna “Tuta Absaluta” da tai wa tumatirin da aka shuka dirar mikiya musamman a Arewacin Najeriya da kuma ruwan sama da aka rinka makawa a baya kamar da bakin kwarya, wanda kuma ya taimaka wajen kashe tumatirin.

You may also like