Turai ‘Yar Addu’a, Matar Shugaban Kasa Mafi Halacci da Nuna Soyayya Ga mijinta


*** Ta fi kowa sanin ba shi da lafiya, amma zurfin ciki irin na cikakkiyar Bafulatanar asali ba a  taɓa jin hakan daga bakin ta ba.
***Kiransa ake yi Gawa Taƙi Rami, amma kara irin ta ƴar asalin jihar Katsina rungumarsa ta yi a matsayin Uban ƴaƴanta.

***Sako shi aka yi a gaba, ana faɗin idan ba zai iya ba ya sauka ya bar mulki, Jonathan ya karɓi ƙasa, amma kasancewarta na mai kishin Arewa ta kafa ta tsare ta ce ba gudu ba ja da baya sai dai Allah Ya karɓa Ya ba shi.

***Mijinta ya shiga wani mummunan yanayi na rashin lafiya amma haka ta hana magautansa damar zuwa inda ya ke saboda fargabar cutar da shi, ta katange shi ta ba riƙa ba shi dukkan cikakkiyar kulawa da soyayya.

***Turai ce Mafi kusanci da mijinta amma ba a taɓa jin ta yi masa katsalandan a sha’anin mulki ba.

***Kafin rasuwarsa ya yi mata wasiyya bayan raina za ki yi rigima da ƴan uwana saboda za su yi zargin ta kwashi dukiyar ƙasa na ba ki. Wannan ya ƙara bayyana jarumtar ta na cewa, ba ta na tare da shi don ya tara mata dukiya ba ne. Tsananin tsantsar soyayya ce ta gaskiya tsakanin Miji da Mata.

***Har ya koma ga Allah ba a taɓa ji ta kira sunan sa kai-tsaye babu girmamawa ƙamar yadda gatsal Aisha ke faɗin, “Shi Buhari…..

Allah Ya Jiƙan Marigayi Umaru Musa Ƴar’adua.

You may also like