Turawa na ci gaba da kyama da wulakanta mata Musulmai


 

A ‘yan watannin da suka shude Kafafan yada labarai na duniya sun yada bidiyo da kuma hotuna da dama game nau’o’in walukanci da mata Musulmai ke fuskanta a nahiyar Turai.

Cin zali da wulakancin da ake nuna wa matan dai na da nasaba da bakar kyamar da Turawa ke yi wa addinin Islama.Kuma matan da aka fi zagi da kai wa hari su ne wadanda ke rufe jikinsu da niqab da  hijabi.

Ga  kadan da cikin halin ha’ula’in da mata Musulmai ke ciki a nahiyar Turai :

Wulakanci na farko dai ya faru ne jim kadan bayan harin da aka kai a Faransa,inda Jaridar Sun ta kasar Ingila ta yi tofi Allah tsine kan shugaban gidan talabijin na Channels 4  Kelvin MacKenzie wadda ta bai wa wata ‘yar jarida Musulma mai sun Fatima Manji damar rufe kanta da lakkabi a yayin da take bada rohoto kan mummunan lamarin.

A kasar Jamus shugabannin wani banki mai suna Sparkasse Bank sun hana wata Musulma ‘yar kasar mai shekaru 20 da haifuwa shiga ma’aikatarsu tare da amfani da karfi a wajen raunana ta.

A kasar Ingila wasu fasinjojin bas sun kai wa wata Musulma naushi tare da jefa ta daga abin hawan.

Haka zalika, a kasar Birtaniyan an sake samun labarin wata Musulma dalibar sakandari mai suna Tasnim Kabir mai shekaru 16 da haifuwa  wanda wani baligi bakar fata ya kai ma ta naushi har sai da suma.

You may also like