Turkiyya: Barazanar Gwamnati Ga Sheikh Gulen


Tun bayan yunkurin juyin mulki da wasu mutane suka yi a kasar Turkiyya, ranar 15 ga watab Yuni, 2015, wanda aka ce wasu manyan sojoji ne da ‘yan barandansu suka kitsa shi. Shirinsu a wancan lokaci shi ne kame manyan biranen kasar, Ankara da Istanbul don ya dawo karkashin ikonsu; sun mamaye manyan gadoji, Majalisar kasa, filayen jirgi da ofisoshin ‘yan sanda. Da alama wadanda suka yi wannan yunkuri ba su shirya ba, ko kuma ba su san abinda suke tunkara ba. Duk da gwamnati ta yi zargin cewa wasu daga cikin manyan sojojin kasar ne suka shirya juyin mulkin, shi ya sa ma aka cafke dubunnan sojoji, wadanda yanzu haka suna hannu.
Mutane sun fara gano yunkurin juyin mulkin da misalin karfe takwas na daren ranar, lokacin da jami’an tsaro suka fara karkatar da jama’a daga bin wasu manyan hanyoyi. Da misalin karfe 10, aka rufe babbar gadar Bosphorous, aka hana kowa motsawa ko nan-da-can.
Kamar yadda gwamnati ta bayyana, akalla sojoji biyar, ‘yan sanda 62, da kuma farar hula 173 suka rasa ransu; sama da mutum 1,500 suka ji munanan raunuka. A rahoton da Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta fitar a Turkiyya, ta ce akalla mutane 208 suka mutu, yayin da sama da 1,400 suka jikkata a daren da aka yi yunkurin juyin mulkin. Daga cikin wadanda suka mutu, akwai mutane 24 da aka yi ikirarin suna da hannu, sai kuma wadanda aka yiwa a ture lokacin da suke kokarin mika wuya.
A karon farko, gwamnatin Turkiyya karkashin Erdogan ta dora alhakin yunkurin juyin mulkin ga mutumin da ta dade tana nema ruwa a jallo, Fethulla Gulen, malamin addinin Musulunci, wanda yanzu haka yake zaman gudun hijra a Saylorsburg, Pennsylbania da ke kasar Amurka tun a shekarar 1999. Wasu daga cikin ministoci sun yi zargin cewa kasar Amurka ta bada gudunmawar a sirrannce don ganin an hambarar da Erdogan ta hanayar yin amfani da gwagwarmayar Gulen.
An bayyana sunan Dakta Henry Barkey, na Tsangayar Ilmi ta Wilson, wanda yana Istanbul lokacin da abin yake faruwa, da cewar shi ne ke kula da yadda juyin mulkin zai kaya. Haka zalika, Janar John K. Campbell, tsohon Kwamandan Rundunar Tsaro Mai Taimakon Kasa da Kasa, shi ma magoya bayan Erdogan sun zarge shi da hannu; jaridu guda biyar na kasar sun rawaito cewa wai yana da hannu a ciki.
Matakan da gwamnatin Turkiyya ta dauka bayan dakile yunkurin juyin mulki, sun nuna yadda aka yi shirin bincike ba tare da bin tsarin doka da oda ba. A wani kalami da Dabid Phillips na tsangayar Kare Hakkin Bil’Adama a jami’ar Columbia ya yi, ya ce Erdogan na neman sakin layi don mayar da Turkiyya karkashin ikonsa gaba daya.
Gwamnatin Erdogan ta bayar da umarnin rufe gidajen jaridu 131, kamfanonin dillancin labarai, gidajen talabiji da rediyo. Baya ga haka, cikin ‘yan kwanaki kadan, gwamnatin ta tsige sama da mutum 104,676 daga wuraren ayyukansu ta kuma tsare 44,206. Ba ta tsaya a anan ba, ta garkame ‘yan jaridu 49, ta kulle makarantu 1,284, jami’o’I 15, kungiyoyi 1,254 tare da asibitoci 35.
Tsagerun matasa masu goyon bayan gwamnati, sun kai wa kungiyar Hizmet farmaki kwanaki kadan bayan faruwar lamarin, a wani gangami da suka yi suna masu barazana ga Hizmet da kuma jagoranta Fethulla Gulen.
Gwamnatin Turkiyya ta fitar da rahoton zargin yunkurin juyin mulki da ta ke yiwa magoya bayan Gulen kamar haka: A ranar 15 ga watan Yuni, tawagar wasu sojoji masu rajin kare Fethullah Gulen, wai sun samu bayanai cewar za a kawar da su a watan Agusta 2015, a lokacin babban taron manyan hafsoshin tsaro kasar nan, saboda haka ne suka yi amfani da karfi don yunkurin kifar da gwamnatin Erdogan domin su kafa tasu gwamnatin. Awanni uku bayan dakile yunkurin juyin mulkin, tashar talabiji ta CNN, ta nakalto Erdogan na fadin sojojin da suka yi wannan yunkurin magoya bayan Gulen ne.
Fethulla Gulen ya fito karara ya yi Allah wadai da yunkurin, a daidai lokacin da labarin lamarin ke yaduwa a duniya. Awannin 31 baya, gamayyar gidan buga takardu na Alliance suka buga jawabin Gulen na yin tir da mutanen da suka so kifar da gwamnatin. Wannan shi ne sakon da Gulen ya fitar, wanda hakan ta sanya sauran kungiyoyi biyo baya wajen nuna bakin cikinsu ga faruwar lamarin. Gidajen jaridu da yawa a fadin duniya sun buga wannan labarin. A wurare da yawa, Gulen ya nesanta kansa da yunkuri; ya jaddada goyon bayansa ga tsarin mulkin dimokradiyya, kuma ya yi tir da mulkin soja. A wata mukala da jaridar New York Times ta buga, Gulen ya ce, “A iya nazarin falsafata – na gamsu da tsarin mulkin Musulunci, wanda yake bai wa kowane mutum damar gudanar da addininsa – amma tsarin mulkin soja ba zai yarda da wannan ba.” Har ila yau jaridar Le Monde ta kasar Faransa, ta rawaito Gulen yana kira ga kasashen duniya kan su sanya baki a yi bincike na gaskiya da adalci, kuma a shirye yake ya bayar da hadin kai.
Bisa zargin da ake yi cewar ko akwai mutanensa a cikin wadanda suka shirya juyin mulkin, duk da cewa ba su ne kanwa uwar gami kan lamarin ba, Gulen ya yi Allah wadai da su, ya ce “Idan har an samu dan kungiyar Hizmet da hannu a ciki, to tabbas ya ci amanarmu, kuma ya yaudare mu.”
Sai dai ga dukkan alamun akwai dalilin da ya sa gwamnatin ta jefa zarginta ga ‘ya’yan kungiyar Hizmet game da balahirar. Mayar da hankalin kan kungiya guda daya, alamu ne da ke nuni da cewar akwai wata manufa a kasa. Ana son baiwa wadansu kungiyoyi kariya ne kawai. Baya ga haka, akwai wadansu dalilan; Erdogan ya ki amincewa ya zama dan amshin shatan gwamnati, kamar yadda wasu malamai ke yi. Har ila yau, ‘yan kungiyar Hizmet sun taka muhimmiyar rawa wajen bankado badakalar cin hanci da rashawa da ta mamaye gwamnatin a shekarar 2013.
Tarihi ya nuna cewar, a duk lokacin da wani shugaban yake neman goyon bayan Musulmi, domin ya shimfida mulkinsa yadda yake so, yana neman hadin kan manyan masu fada a ji ne, saboda bangarancin siyasa ko addini. Domin cimma burinsa na zamowa gwarzo a tsakanin jama’a, mutane irin Erdogan suna neman hadin kan manyan malamai, su zamo karkashinsu, suna juya su yadda suke so – har su rika yaba musu a bainar jama’a kan ayyukansu.
A lokuta da yawa, wadanda suka bijirewa gwamnati suna fuskantar barazanar kisa, dauri ko azabtarwa. Game da tsamar da ke tsakanin Erdogan da Gulen, ita ma hakan ta ke, babu bambanci; yana son yin amfani da shi ne kawai. Duk da cewa tsarin mulkin Turkiyya ya bai wa kowane bangaren addini ‘yancin kansa na tsayawa zabe, amma Erdogon yana samun kuri’u ta hanyar yin amfani da farfagandar addini, yana lashe zabe. Ba ya jure suka daga bangarorin Musulmi.
Akwai bangarorin adawa masu yawan gaske a Turkiyya, amma me zai sa idanun Erdogan su fi karkata kan Gulen, ko saboda ya zamar masa karfen kafa ne? Erdogan zai iya murkushe da yawa daga cikin masu adawa da shi. Zai iya cewa Kemalist suna da matsala a addinance. Zai iya cewa Alebis suna takun saka tsakanin bangaren Sunni sannan sun zamo karnukan farauta da turawan yamma ke amfani da su. Ba kamar Gulen ba, domin Gulen ya fara adawarsa ne daga lokaci da aka bankado badakalar cin hancin da rashawa, da kuma sauya tsarin gudanar da harkokin mulkin kasar.
Fethullah Gulen mutum ne da ya tsaya kai da fata wajen sukar lamirin gwamnati, ya ki amincewa ya zama dan amshin shata. Yana kira kan a samar da daidaito a mukaman gwamnati. Idan har Erdogan ba zai iya gabatar da wata kwakkwarar shaida kan inda Gulen ya kauce daga tafarkin addini ba, to ba zai iya murmushe gwagwarmayar da ya dauki shekara da shekaru yana yi ba.
Gulen yana bin tafarkin addini Musulunci ba bisa ra’ayin wani ba, yana kuma kallon lamurra da idon basira don bambance aya da tsakuwa, kana kowa ya san ba haka kawai ya fara caccakar gwamnati ba, hasalima, ba ya tsalma baki cikin sha’anin mulki har sai lokacin da aka bankado badakalar cin hancin da rashawa a gwamnatin Erdogan da kuma irin tsarin da gwamnatin ta dora kanta a kai, wanda sam babu gaskiya da adalci a ciki wajen nada-naden mukamai.
Tun da har Erdogan ba zai iya gabatar da wata babbar shaida cewa Gulen yana da matsala kan tafarkin addini, kuma koda yaushe yana caccakarsa ba bisa doron gaskiya ba, sam bai kamata gwamnatinsa ta yi yunkurin hana Gulen aiwatar da aikace-aikacensa na alheri ba.

You may also like