Turkiyya na bayar da taimako wajen samar da zaman lafiya a Yaman


 

Ministan tattaunawar sulhu a kasra Yaman Yasir Abdullah Al-Ruayn ya sanar da cewa, Turkiyya na bayar da gudunmowa sosai wajen dawo da zaman kafiyar kasarsu.

Kamfanin dillancin labarai na Yaman SABA ya bayyana cewa, minista Al-Ruayn ya gana da jakadan Turkiyya a birnin Sana Levent Eler.

A yayin tattaunawar, Al-Ruayn ya ce, sun gamsu tare da jin dadi game da taimakon da Turkiyya ke basu don dawo da zaman lafiyar kasar.

Al-Ruayn ya ci gaba da cewa, tun bayan fara tattaunawar dawo da zaman lafiya a Yaman Turkiyya ke bayar da gudunmowa, inda ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su bayar da tasu gudunmowar don dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yaman.

Jakadan Turkiyya a Sana Levet Eler kuma ya ce, Turkiyya za ta ci gaba da bayar da goyon bayan ga halartacciyar gwamnatin Abdurrab Hadi Mansur kuma za ta ci gaba da kasancewa tare da Yaman a koyaushe.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like