Turkiyya ta ci gaba da lugudan wuta kan Kurdawa


Screen Shot 2016-08-29 at 9.23.27 PM

 

Turkiyya ta sha alwashin ci gaba da lugudan wuta kan mayakan Kurdawa a Siriya matsawar ba su fice zuwa yankin gabashin kogin Euprathe ba.

Ministan cikin gidan na Turkiyya Mevlüt Cavusoglu ne ya sanar da hakan a gaban manema labarai inda ya yi karin bayani yana mai cewa:

“Dole mayakan kungiyar ‘yan awaren Kurdawa su janye daga gabashin kogin Euprathe kamar yadda Amirka ta yi alkawarin cewa za su yi ko kuma dai mu ci gaba da harar su.”

Kamfanin dillancin labaran Turkiyyar na Anadolu ya ruwaito cewa ko a wannan Litinin jiragen yakin Turkiyyar sun yi lugudan wuta kan mayakan ‘yan awaren PKK a yankin Gara na arewacin Iraki. A ranar Larabar da ta gabata ne dai Turkiyyar ta soma kaddamar da harin da ta yi wa lakabin garkuwar Euprathee kan mayakan Kurdawan da ma na kungiyar IS a Siriya.

Sai dai kasar Amirka ta bakin manzon Shugaba Obama a wajen rundunar hadin gwiwa da Amirka ke jagoranta a yaki da kungiyar IS wato Brett McGurk ya bayyana hare-haren da Turkiyya ke kaiwa kan kawancan mayakan Larabawa da na Kurdawa da cewa ba su dace ba. A kan haka ya yi kira ga bangarorin biyu da su dakatar da buda wuta.

You may also like