TURKIYYA TA DAU ALWASHIN KALUBALANTAR AMURKA KAN BIRNIN QUDUS 



Shugaban Kasar Turkiyya, Tayyib Erdogan ya bayyana Isra’ila a matsayin kasar ‘yan ta’adda inda ya yi alwashin daukar duk wani mataki na kalubalantar Amurka na amincewa da birnin Jeruslem a matsayin Babban birnin kasar Isra’ila.

Ya ce, Musulmi ba za su taba bar wa Isra’ila birnin Jerusalem inda ya nuna cewa Amurka ba ta yi wa Falasdinawa adalci ba na mikawa Isra’ila birnin Qudus alhali kuma kowa ya san yadda sojojin Isra’ila ke hallaka kananan yaran Falasdinawa.

A dayan bangaren kuma, kasar Lebanon ta yi kira ga kasashen Larabawa kan su yi tunanin kakaba wa Amurka takunkuman karya tattalin arziki don hana ta mayar da ofishin jakadancinta zuwa Birnin Jeruslem daga Tel Aviv. Tun da farko dai, ministocin Harkokin wajen kasashen Larabawa sun yi Allah wadai da matakin da Amurka ta dauka kan birnin Jerusalem.

You may also like