
Asalin hoton, Getty Images
Uefa za ta yi bincike kan Barcelona, sakamakon kudin da ta biya tsohon mataimakin shugaban kwamitin rafli a Sifaniya.
Tuni hukumar ta nada jami’in da zai yi bincike kan kudin da ake zargin Barcelona ta yi don ta samu sakamakon wasannin da zai amfane ta.
An shigar da karar Barcelona kan tuhumar cin hanci da bayar da rahoton karya da aikata rashin gaskiya.
Masu shigar da kara na tuhumar Barcelona da biyan fam miliyan 7.1 ga Jose Maria Enrique Negreira da kamfaninsa Dasnil 95.
Barcelona wadda ta musanta aikata ba daidai ba ta ce ta biya kudin ga Dasnil 95 tsakanin 2001 zuwa 2018.
Uefa ta ce: “Ta nada jami’in da zai binciko ko Barcelona ta karya dotar hukumar kan kudin da ake zargin ta biya Caso Negreira.”
Wani gidan rediyo ne mai suna Ser Catalunya ya bayar da rahoton biyan kudin daga nan mahutuntan karbar haraji suka fara bibiyar Dasnil 95.