Ukraine: NATO ta bukaci a kara shiri | Labarai | DWJens Stoltenberg ya yi wannan furici ne a wata hira da ya yi da kamfanin yada labarai na kasar Jamus da ake kira Funke, inda ya ce a mafi yawan lokuta yaki na dadewa fiye da lokacin da ake tsammani, don haka ya zama wajibi kasashen kungiyar su shirya damarar yin dogon yaki a Ukraine. To sai Stoltenbergya ce kawancen na NATO na son zaman lafiya, to amma abin la’akari shi ne idan Shugaba Volodymyr Zalensky da ‘yan Ukraine suka ajiye makamai to kasarsu za ta shafe daga doron duniya. Wannan gargadi na sakataren kungiyar ta NATO na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Kiev ke ci gaba da kai farmaki domin fatattakar takwarorinsu na Rasha daga yankunan Ukraine da suka mamaye.

Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like