
Asalin hoton, TELEGRAM: HOREVICA / ZSU STRATCOM
Ukraine ta ce akalla sojojin Rasha 400 ne suka rasu sakamakon hari da makamai masu linzami da ta kai a lardin Donetsk da Rasha ta mamaye.
Sai dai jami’an Rasha sun ce sojoji 63 aka kashe a harin.
Amma har yanzu babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin kasashen biyu.
Harin da aka kai a jajibirin Kirisimeti a birnin Makiivka inda dakarun Rasha ke zaune ya samu wani gini
Can kuma a birnin Kyiv, an yi luguden wuta inda hukumomin Rasha ke ci gaba da kai hare-hare.
A cikin wata sanarwa, gwamnatin Rasha ta ce harin da Ukraine ta kai mata , an kai shi ne da makaman roka guda shida kirar Amurka.
Daniil Bezsonov, wani babban jami’in Rasha ya ce an kai hare-haren a tsakar dare na ranar sabuwar shekara.
“Wannan babban nakasu ne Rasha,” in ji Bezsonov.
Vladimir Solovyov, wani mai gabatar da shiri a Rasha ya wallafa a shafin Telegram cewa “rashin babba ne … sojojin sun kai 400”.
Sai dai a cewar dakarun Ukraine, sojojin Rasha 300 sun jikkata baya ga 400 da aka kashe.