Ukraine za ta samu karin tallafi daga Jamus | Labarai | DWMinistan tsaron Jamus Boris Pistorius ne ya sanar da hakan a wannan Litinin (18.09.2023 inda ya ce za a bai wa Kiev wani sabon kunshin taimako da ya ta tashi a miliyan 400 na yuro domin kara mata karfin soja.

Karin bayani: Jamus za ta saya wa Ukraine makamai

To sai dai yayin da yake sanar da wannan sabon kunshi na taimakon, ministan ba yi ba karin bayani kan batun aike wa Ukraine da makamai masu linzami masu cin dogon zango samfarin ”Taurus” kamar yadda mahukutan Kiev suka bukata.

Karin bayani: Jamus za ta tallafa wa Ukraine da tankokin yaki

Wanda tallafi zai karawa dakarun Kiev kwarin guwiwa kan farmakin suka kaddamar a karshen watan Juni domin fatattakar dakarun mamaya na Rasha da suka karbe iko da yankuna da dama na kasar.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like