Ukraine za ta shiga kungiyar tsaro ta NATO | Labarai | DW



Shugaban na Ukraine ya ce hakan wani mataki na tabbas ne da kasar ta dauka domin nuna himmatuwarta ga bukatar shiga kungiyar.

Mr. Zelenskyy ya ce ba zai taba yin wata tattaunawar sulhu da Rasha ba, muddin dai Vladimir Putin ne ke shugabantar kasar.

Ya yi alkawarin cewa shugaban kawai a Rasha da zai yi zaman sulhu da shi, sai wani sabon ba kuma na yanzu ba.

Kafin wannan sanarwa ta shugaba Zelenskyy dai, sai da wasu jiga-jigan majalisar tsaron kasar suka yi wata ganawa a game da abin da Rasha ta yi na ayyana shigar da wasu yankunan Ukraine a cikinta a ranar Juma’a.



You may also like