
Asalin hoton, Other
Masana shari`a a Najeriya, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan umarnin da kotun kolin kasar ta bai wa bangarorin da ke shari’a a kan wa’adin da Babban Bankin kasar ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun naira.
Masanan na ganin cewa umarnin kotun na da harshen damo ma’ana yana da sarkakiya.
Masanan sun ce rashin fayyace matsayin kowanne bangare da kotun ta yi shi ya sa suke kallon umarnin kotun a matsayin mai harshen damo.
Barista Sa’idu Muhammad Tudun Wada, lauya ne mai zaman kansa a Najeriya, ya kuma shaida wa BBC cewa, a yanzu ‘yan Najeriya sun shiga cikin rudani saboda rashin fayyace matsayin kowane bangare da kotun kolin ta yi, wanda haka zai sa jihohin da suka shigar da kara za su iya fassara umarnin kotun na kowa ya tsaya a matsayarsa har zuwa ranar da kotun za ta sake zama a matsayin umarnin hana dakatar da mutane daga mu’amala da tsoffin kudade.
Ya ce, “Ita kuma gwamnati za ta dauka cewa umarnin da CBN ya bayar na cewa a dakatar da karbar tsoffin kudade yana nan, to gaskiya bisa la’akari da wannan fassara da wadan nan bangarori za su yi wa umarnin kotu ba karamin jefa mutane cikin rudani aka yi ba.”
Tun da farko kotun ta umarci Babban Bankin da ya jingine batun wa’adin da ya bayar, amma daga baya sai ta umarci bangarorin biyu da ke gaban nata, wato da gwamnatocin jihohin da suka kai karar da kuma bangaren gwamnatin tarayya cewa kowa ya tsaya a inda yake har zuwa ranar 22 ga watan Fabrairun 2023.
Ana su bangaren, wasu masana shari’ar, sun ce bisa la’akari da irin abubuwan da ke faruwa ya nuna cewa ita kanta gwamnatin tarayya bata bi umarnin kotu ba tun da farko da ta ce Babban Bankin ya jingine batun wa’adin da ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun naira daga ranar 10 ga watan Fabrairun 2023 sai kuma maganar kara shigar da wasu jihohi cikin shari`ar ta taso.
Barista Abba Hikima, shima lauya ne mai zaman kansa, ya kuma shaida wa BBC cewa, idan har ya tabbata bankuna basa karbar tsoffin kudade, to ya fito fili ke nan Babban Banki bai yi aikinsa ba saboda ai kotu ta ce kada a dakatar da karbar kudaden.
Ya ce, ‘”Akwai bukatar CBN kasancewarsa wani bangare na gwamnatin tarayya ya aiwatar da umarnin da aka bai wa gwamnatin tarayya ta hanyar bawa bankuna umarnin ci gaba da karbar tsoffin kudade.”
A Najeriyar dai a kan koka da yadda wasu kan yi wa umarnin kotu karan-tsaye, musamman ma a matakin kananan kotuna da manya, har takan kai ga fuskantar fushin kotunan.
To amma bijirewa umarnin kotun karshe wadda tafi kowacce daukaka wato kotun koli, akwai babban hadari a ciki a cewar Barista Sa’idu Tudun Wada.
Ya ce, “Illar rashin bin umarnin kotu, shi ne yana zubar da kima da daraja da kuma mutuncin da kotu ke da shi, sannan zai bude dama na kowa ya yi yadda yake so.”
Baristan ya ce, don haka rashin bin umarnin kotu na janyo fitintinu a kasa.
A ranar 15 ga watan Fabrairun 2023, ne dai kotun kolin Najeriyar ta dage zaman sauraron karar da wasu gwamnatoci uku suka kai gaban nata zuwa ranar 22 ga watan domin bai wa wasu gwamnatocin jihohin da su ma suka nemi shiga cikin karar ta yadda za su dunkule wuri guda dama.
Batun daina amfani da tsoffin kudi a Najeriyar ya hassala ‘yan kasar da dama har ta kai ga yin zanga-zanga a wasu sassan kasar sakamakon halin matsi da suka shiga saboda ana fama da karancin sabon kudin yayin da bankuna da mutane da dama kuma suka daina hada-hada da tsohon kudin.