UNESCO: Isra’ila ba ta da ikon yin kaka gida a Masallacin Aksa


 

 

Hukumar Cigaban Ilimi da Raya Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta bayyana cewa, masallacin Aksa mai albarka ba shi da alaka da Musawiyanci.

Ministocin Harkokin Waje na Hukumar ne suka jefa kuri’a kan batun inda 24 suka yi nasara kan guda 6.

Akwai mambobi 26 da ba su jefa kuri’a ba inda wasu biyu kuma ba su halarci zaman ba baki daya.

Kudirin da Hukumar ta fitar ya soki Isra’ila tare da cewa, ba ta hakkinkula o shugabantar Masallacin Aksa da ke Kudus, kuma guri ne Ibadar Musulmai, Kiristoci da Musayawa.

Hukuncin ya kuma sanar da cewa, Masallacin Aksa na da alaka ta kusa da Addinin Musulunci, kuma ba a bayyana cewa, Isra’ila da Musawiyanci na da alaka da shi ba.

Faransa ba ta jefa kuri’a ba inda Amurka, Jamus da Birtaniya na daga cikin kasashen da suka ce a a.

A ranar Litinin mai zuwa Majalisar Gudanarwar UNESCO mai mambobi 58 za ta sake zama tare da jefa kuri’a a kan batun.

You may also like