UNICEF –  YARA MILIYAN 5 KEYIN HIJIRA A DUNIYA


Asusun kula da yara kanana na MDD UNICEF ya ce kusan yara miliyan 50 suke barin kasashensu na asli domin yin hijira a cikin wasu kasashe saboda dalilan yake-yake, da kuma wasu matsalolin da kan tasowa.
Asusun ya ce a shekara ta 2015 da ta wuce kimanin kishi 45 cikin dari na yaran ‘yan gudun hijira da ke a karkashin kulawar MDD ‘yan asilin kasashen Siriya ne da Afganistan wadanda yaki ya sa suka baro kasashensu.

Mataimakin daraktan asusun ya ce akwai bukatar a daina raba yara da iyayensu akasari ‘yan ci rani masu neman mafaka.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like