
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na tunanin sayen ɗan wasan gaban Atletico Madrid mai shekara 31 Antoine Griezmann, wanda ya lashe kofin duniya a 2018 kuma a halin yanzu zai buga wasan karshe na kofin duniya a bana. (Mediafoot – in French)
Real Madrid ta shiga jerin masu neman ɗan wasan PSV Eindhoven da kuma Netherlands Cody Gakpo wanda tuni aka soma alaƙanta shi da Manchester United da Newcastle. (Mirror)
Manchester United na son sayen Gakpo wanda ya ci ƙwallaye uku a gasar cin kofin duniya, domin ya maye gurbin Christiano Ronaldo a watan Janairu. (Telegraph – subscription required)
Wolves na son sayen ɗan wasan da ya ci gasar zakarun nahiyar Turai sau biyar wato Isco daga Sevilla. Ɗan wasan mai shekara 31 wanda yake a Real Madrid a baya wanda kuma ya buga wa ƙasarsa Sifaniya sau 38 akwai wasu kulob din da ke nemansa kamar Juventus da Napoli da Aston Villa. (Todofichajes – in Spanish)
Watan Janairu zai zama wata na gwagwarmaya ga Wolves waɗanda suke son sayen sabbin ƴan wasa har shida idan aka bude kasuwar sayen ƴan wasa. Sabon kocin kulob ɗin ɗan Sifaniya Julen Lopetegui ya bayyana cewa yana son ƙara ƴan wasa daga Birtaniya kulob ɗin. (Times – subscription required)
Haka kuma Wolves ɗin na son sayen ɗan wasan bayan Manchester United Aaron Wan-Bissaka mai shekara 25. (Express & Star)
Rahotanni na cewa wanda Liverpool da Tottenham ke hari Sofyan Amrabat mai shekara 26 ya tayar da manyan kulob daga barci sakamakon irin rawar ganin da ya taka a Morocco a gasar cin kofin duniya. Amrabat yana buga wa Fiorentina wasa. (De Telegraaf, via Talksport)
Everton kuwa za ta shiga cikin masu neman ɗan wasan Ajax mai shekara 22 kuma ɗan ƙasar Ghana Mohammed Kudus a watan Janairu. (Ekrem Konur on Twitter)
Haka kuma ɗan wasan tsakiyar Faransa da Juventus mai shekara 27 Adrien Rabiot ya nuna sha’awar komawa Barcelona. (Sport)
Akwai yiwuwar Cristiano Ronaldo mai shekara 37 ya soma shirin sanar da ritayarsa daga ƙwallo, kamar yadda Patrice Evra ya bayyana. A halin yanzu Ronaldo ba shi da kulob tun bayan da ya bar Manchester United a watan Nuwamba. (Sky Sports)