United ta ragargaji Chelsea ta samu gurbin Champions League



Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta doke Chelsea 4-1 a kwantan wasan Premier League da suka kara ranar Alhamis a Old Trafford.

Minti shida da take leda Casemiro ya ci wa United kwallon farko, sannan Anthony Martial ya kara na biyu daf da hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Bruno Fernandes ya ci na uku a bugun fenariti, sannan Marcus Rashford ya zura na hudu a raga a fafatawar.

Daga baya ne Chelsea ta zare daya ta hannun Joao Felix daf da za a tashi daga karawar ta hamayya.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like