United za ta buga wasan sada zumunta da Leeds a Oslo a Yuli



Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United za ta buga wasan sada zumunta da Leeds United a Oslo, domin gwada ‘yan wasan da za su buga mata kakar badi ta 2023/24.

Za su kara ranar 12 ga watan Yuli a filin Ullevaal a Oslo, kuma na farko da za su fuskanci juna a Norway.

Haka kuma karawar dama ce ga United, domin shirin buga wasanni hudu a Amurka, duk domin tsare-tsaren yadda za ta taka rawar gani a badi.

Wannan shi ne karo na hudu da United za ta kece raini a filin Ullevaal, bayan wasan sada zumunta a 2017 a Valerenga da 2019 a Kristiansund.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like