United za ta kawo Boubakar, Man City ta yi wa Madrid kutse kan BellinghamVincent

Asalin hoton, OTHER

Jaridar Sport ta ruwaito cewa dan wasan gaban Barcelona da Netherlands Memphis Depay na son komawa Manchester United, shekaru shida bayan ya bar Old Trafford.

Manchester City kuwa ta shirya karfafa tsakiyarta badi, kuma dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jude Bellingham na cikin wadanda za ta yi amfani da su wurin cimma burinta.(ESPN).

Tuni kungiyoyin Madrid da Liverpool suka nuna sha’awar sayen matashin mai shekaru 19, kuma Dortmund na son ya tabbatar mata idan yana son ci gaba da wasa a kungiyar a kaka ta gaba.(90min).

Ita kuma Chelsea na ci gaba da tattaunawa da Shakhtar Donetsk kan dan wasan gabanta Mykhailo Mudryk.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like