
Asalin hoton, Getty Images
Asha Devi da makwaftanta sun yi murna lokacin da aka zartar da hukuncin rataya ga mazan hudu ranar 20 ga watan Maris 2020
A rana mai kamar ta yau, shekaru 10 da suka wuce aka yi wa wata matashiya fyaden taron dangi, aka ci zarafinta a motar bus a babban birnin Delhi na kasar Indiya.
Kwanaki bayan nan ta mutu sakamakon munanan raunukan da ta ji.
Gabanin rasuwarta, lokacin da take kwance a asibiti cikin halin rai-kwa-kwai mutu-kwa-kwai, ‘yan jarida suka fitar da sunanta da Nirbhaya mara tsoro.
Lamari ne da ba a saba da shi ba a Indiya wato fadar sunan wadanda aka yi wa fyade, don haka sai ta yi tambari lokaci guda.
Labarin ya ja hankalin duniya, an dauki makwanni na zanga-zangar matsawa gwamnati mabar daukar hukunci mai tsauri kan cin zarafin mata.
An tsinci gawar wanda ya jagoranci fyaden wato direban motar bas din a dakin da ake tsare da shi a gidan kaso watanni kalilan bayan aikata laifin.
A watan Maris din 2020 aka rataye sauran mutum hudun, yayin da aka saki dayan bayan shafe shekaru uku gidan kaso.
Lamarin da ya sauya yadda ake tattaunawa kan batun cin zarafin mata, da bai wa mata taimako fiye da wanda Asha Devi mahaifiyar Nirbhaya ta samu.
Matar aure ce mai saukin kai da ta sadukar da rayuwarta wajen kula da ‘ya’yanta da iyalinta, amma abin da ya faru ga ‘yarta karfi da yaji ya mayar da ta mai fafutuka da gangamin wayar da kan mata da ‘yan mata kan yadda za su kare kansu.
Ta fara gangamin da neman yi wa ‘yarta hakki, a yanzu kuma ga dukkan mata da ‘yan matan kasar.
Shekaru biyu da suka gabata, a ranar da aka cika shekaru takwas da yi wa ‘yarta fyade, watanni kadan bayan rataye mutne hudun da ak samu da laifi, ta fara wni sabon gangami mai taken ”Adalci ga dukkan matan da aka yi wa fyade.”
“Ta wannan hanyar ne zan girmama ruhin ‘yata,” in ji ta. Duk da ciwon kafar da take fama da shi, da dingishi da ke bukatar zuwa asibiti kusan a kowacce rana domin a yi mata gashi.
Jajirtacciyar uwar mai shekara 56 tana jagorantar wata karamar kungiya dauke da kyandira inda suka shafe kawanni biyar su na yi maci a gundumar Dwarka da ke birnin Delhi.
Asalin hoton, Getty Images
Bakin cikin da Asha Devi ta samu kan ta a ciki ya ja hankalin kafafen yada labarai a ciki da wajen Indiya har da gidajen talbijin
Mutanen na neman a yi wa matashiyar ‘yar shekara 19 adalci kan fyaden gayya da aka yi mata da kashe ta shekaru 10 da suka gabata.
Uku daga cikin mazan da ake zargi, sun sha bayan kotun kolin Indiya ta ce babu wasu kwararan shaidu da za su tabbatar sun aikata lafin.
Asha Devi da mutanen suna zanga-zangar ne saboda sake nazarin hukuncin da babbar kotun kasar da zartar na sakin mutanen.
Mutanen suna rike da allon da aka rubuta ‘Ba a taba mantawa da fyaden da aka yi na Chawla ba”.
Kwanaki n farko na zanga-zangar babu mutane sosai, amma a hankali mutane suka fara fitowa, wasu ranakun mutane 15 ne ke fitowa amma haka muke yi ba za mu karya ba,” In ji Asha Devi, inda ta ce suna bukatar kotu ta sake nazari kan hukuncin.
Dukkan wadanda ake zargi da aikata fyaden, sun koma gidan kaso.
Kwana guda bayan kotun koli ta yanke hukuncin, Asha ta je domin ganawa da iyayen wadanda aka yi wa ‘ya’yansu fyade.
“An min adalci, ba na bukatar zuwa na yi wani abu, amma ba zan manta yadda nake zuwa na zuna a kofar shiga kotu ni kadai ba.
Ina ganin bai kamata hakan ta sake faruwa ga wani ba, sai na je na zauna tare da iyayenta na taya su kuka da jimami,” in ji ta.
A baya-bayan nan, ta taimaka da fitar da wata sanarwa da aka yada a shafukan sada zumunta da ke bukatar a yi wa Bilkis Bono adalci, bayan maza 11 sun yi mata fyaden gayya tare da kashe yawancin ‘yan uwanta.
Daga bisani kuma aka sake su ba tare da wani hukunci daga gwamnatin jihar Gujarat ba.
Asusun da Devi ta kafa domin tunawa da ‘yarta, na taimaka wa wadanda aka yi wa fyade, da shawarwari da tallafin asibiti da yadda za su kaucewa faruwar hakan nan gaba.
Asusun na dauke da tsofaffin lauyoyi, da tsofaffin ‘yan sanda da ma’aikatan sa kai da tsofaffin alkalai.
Shekarun da suka gabata, sun taimaka wa gwamman iyalai. Yawan ganin ta da hukumomi da ‘yan sanda ke yi na sanya su daukar matakin gaggawa.
Amma Asha ta ce shekaru 10 bayan mutuwar ‘yarta, babu abin da ya sauya.
A shekarar 2012 aka kai wa Nirbhaya hari, an samu karin laifukan fyade 24,923 a Indiya.
A shekarar 2021, da ta zamo ta karshe da aka fitar da kididdigar aikata laifuka, adadin kan fyaden ta karu 31,677.
”Ana yin dokokin ne a takarda ba tare da aiwatarwa ko zartar da su ba, ana yin alkawarin da ba a cikawa” in ji Asha Devi.
“Idan aka ci gaba da tafiya a haka, babu wani adalci da za a iya yi nan gaba.”
Asalin hoton, Getty Images
An yi ta kiraye-kirayen a rataye wadanda suka yi ba Nirbhaya fyade
Sanin halin da ta samu kanta a ciki, na daga cikin abin da ya bi wa Asha Devi kwarin gwiwar fara gangamin, yakin da ta shafe shekaru tana yi da fannin shari’a, bakin ciki da bacin rai irin na uwa da ta rasa ‘yarta abin takaicin kuma na wulakanci.
Shekaru 10 bayan nan, abin da ya faru a ranar Lahadin ba zai taba bacewa a zuciyarta ba.
“16 ga watan Disamba, rana ce da bai kamata kowa ya ganta ba, ranar bakin ciki,” in ji ta.
Matashiyar ‘yarta mai shekara 23 ta kammala gwajin da ake musu na likitar gashin kashi, an gayyace ta tattaunawar neman aiki a asibitoci da dama a dan tsakanin, daya daga ciki sun amince su yi aiki da ita a matsayin likita mai son horon aiki.
“Har an bata katin shaidar aiki da asibiti, za kuma ta fara ranar Litinin.
Ta shaida min ‘Ma ‘yarki yanzu ta zama.’ ta fada cike da farin ciki.”
A ranar Lahadin da rana, bayan ta bar gida, ta yi wa mahaifiyarta alkawarin dawowa gida bayan awa biyu zuwa uku.
Lokacin da Asha Devi ta kara ganin ‘yarta, sa’o’i kadan kwance take magashiyyan cikin jini an saba mata kamanni.
Lokacin hira da gidan talbijin din kasar, ta bayyana ciwukan da ke jikin ‘yarta da ”ta yi kama da wadda aka kwato ta daga bakin kura.”
Likitoci sun ce sun rasa abin yi, sun rasa inda za su dinke, da wankewa ko shafa magani.”
An yi wa matashiyar fyaden gayya tsakanin direban motar bus da wasu maza biyar, abokin ta namiji da suke tare an lakada masa dukan kawo wuka.
Tsirara aka yi musu, aka yasar a gefen hanya. Wasu da suka gan su ne suka taimaka aka kai su asibiti bayan kiran ‘yan sanda.
”Abin da ya faru da ita cin zarafi ne da rashin imani, da azabar da ta sha, da tuni ta mutu tun a ranar, amma sai bayan kwanaki 12 ta rasu,” in ji mahaifiyarta.
Sun ba ta suna Nirbhaya, saboda kwazonta. “Babban abin dan sani” game da rayuwarta”, ta fada cikin gunjin kuka da share hawaye.
Shi ne lokacin da ta tuna rokon da ‘yarta ta dinga yi a lokacin da ta ke ‘tuna yarta a raye, tana share hawaye, ta ce bakin cikinta shi ne rashin ba ta ruwan sha da ta yi ta rokon a ba ta, amma ko cokali daya ba su bata ba.”
“Na yi ta tunanin me ye laifin ‘ya ta? Me yasa za ta yi mutuwar wahala? Ina kallon yadda take shan wuya, na kuma samu dan kwarin gwiwa daga gare ta.
Na kuma yi mta alkawarin zan kwatar mata ‘yanci. Abin da kawai nake bukata shi ne mazan fada suka aikata hakan su fuskanci hukunci.
Yayin da aka fara shari’ar Ash Devi ba ta taba fashin halarlar zaman shari’ar ba, dare da rana, ruwa da iska baya hana ta zuwa.
“Ban taba fashin zuwa kotu ba, wata rana ak ki bari na je kotun daga gida, karfin tuwo na sanya na tafi tun daga lokacin komai na ke yi da zarar lokacin zuwa ya yi, ba na fashi,” in ji ta.
Asalin hoton, Getty Images
Duk da jan hanklin da batun ya ja, an kwashe shekara bakwai na shari’a domin karkare zartarwa da mau laifin hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Asha Devi ta ce ta kadar da komai na ta domin yin nasara, kuma ba ta karaya ba.
An haifeta a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya, ”Dole na daina zuwa makaranta jim kadan bayan kammala firamare saboda makarantar sakandren na da nisa daga gidanmu.”
Don haka ta sha wuya kafin ta fahimci dokoki da hukunce-hukuncen shari’a, da koyon yadda ake taron manema labarai.
Sai dai mummunan hali da bakin cikin da uwa ke shiga kan halin da ‘yarta ta kasance ya dauki hankalin kafafen yada labarai musaman talbijin, hakan ya dauki hankalin ‘yan kasar da dama daga lauyoyi, zuwa’yan siyasa da fitattun mutane da masu fafutuka, kowa na son taimakawa kan shari’ar.
An yi zanga-zanga a daukacin Indiya, tare da bukatar a yanke hukuncin kisa kan wadanda suka aikata fyaden.
Amma da kotun koli ya sanar da hukuncin a watan Satumbar 2017, iyalan mutnen da lauyoyinsu suka yi kokarin dakatar da hukuncin ta hanyar sake bude shari’ar da kira ga hukumomi su sake nazari.
Masu fafutuka sun ce hukuncin kisa ba ya rage aikata laifin, yana janyo karuwar wasu mutanen su mutu saboda masu laifi na kokarin kauda duk wata shaida da za ta nuna da hannunsu a aikata laifin.
Sai dai Asha Devi ta ce a nata bangaren ta samu kwanciyar hankali da aka zartar da hukuncin.
Asalin hoton, Getty Images
Matar daya daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya, ta yanke jiki t fadi lokacin da kotu ta yi watsi da bukatar hakan.
Yayin da shari’ar ta karde m’aikatar shari’ar Indiya, ta janyo sake duba wasu dokoki kan cin zarafin mata ta hanyar lalata.
Asha ta ce wani lokacin mutane su na fada ma ta,”’yar ki ta mutu ba za ta dawo ba, ta bar duniya , ki na wahalar da kan ki.”
Amma kullum uka fada min haka, ba su amsa da cewa na ke; ”Ba zan karaya ba”.
Ta ce tallafin da ta dinga samu daga mutane da bata kwarin gwiwa ya wuce tunaninta. Abin da ya sanya ta ce sai ta ga kwar uwar daka, sai ta kwatarwa ‘yar ta hakki.
”Wani lokacin na kan karaya, to tsoro ya kama ni amma daga bisani na gyagije,” in ji Asha.
“Nakan yi tunanin, idan ba a rataye mazan ba, me za a yi musu? Ta yaya mutane za su shaida hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifi irin wannan?
Shari’ar ta fuskanci kalubale da dama, da salo iri-iri, an kuma dauki lokaci ana yi, ”ba na iya bacci ko cin abinci, ba na samun walwala da nutsuwa.
Amma ranar 20 gawatan Maris 2020 da misalin karfe 5:30 na safiya aka rataye mutanen, ba zan manta da ranar ba a rayuwata, na samu nutsuwa da kwanciyar hankali, saboda an aiwatar da hukuncin daidai da laifin da suka aikata,” in ji Asha.
Wata mai fafutukar kare hakkin mata da daidaito, da suke tare da Asha a wannan lokaci mai suna Shruti Singh, ta bayyana yadda daren ranar ya kasance.
”Mun isa gida bayan dawowa daga inda aka zartar da hukuncin, mun koma gida tare da tas hoton Nibharya a gaba, a yanzu mu na da kwarin gwiwar tsayawa kusa da hotonta.
”A yanzu za mu iya kallon fuskarki, saboda ba mu kunyata ki ba”, in ji Asha Devi.