Uwargidan shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta ce ‘yan gudun hijra na Bukatar Taimakon Gaggawa


 

Uwargidan shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta ce ‘yan gudun hijra da rikicin Boko Haram ya tilastawa ficewa daga gidajensu a arewa maso gabashi kasar na bukatar taimakon gaggawa.

Hajiya Aisha ta bayyana hakan ne yayin da ta ke ganawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka yayin da ta ke wata ziyarar kwanaki hudu a birnin Washington D.C.“Halin da su ke ciki ya wuce gwamnatin Najeriya ita kadai ta tallafa musu, dole ne mu nemi taimako.” In ji uwargidan shugaban kasar Najeriya.

Aisha ta na bayani ne dangane da maksudin ziyarar ta su wacce za ta hada har da neman hadin kan kungiyoyi da suka kware a fannin sulhu da wanzar da zaman lafiya.

“Jiya (Alhamis) mun je cibiyar wanzar da zaman lafiya a nan Amurka inda wasu mutane suka zo su ka same mu anan muka tattauna da su.” In ji ta.

Ta kara da cewa a irin tattaunawra da su ka yi da mutanen sun gaya musu cewa ba wai kudade su ke nema ba.

“Muna neman a taimaka mana, kamar yanzu alal misali, yunwar da yara su ke fama da ita, ba wai sabon abu ne ba a arewacin Najeriya, saboda yara wadanda aka haifa ba sa wuce shekara biyar, saboda suna mutuwa daga cututtukan da yunwa ke haifarwa.”

Baya ga wannan batu, uwargidan shugaban ta tattabo wasu batutuwa ciki har da takaddama da ke tsakaninsu da gwamnan Eikiti Ayo Fayose.

You may also like