A yau Litinin ne wa’adin kwana 45 da babbar kotun taraiyar Nijeriya ta yanke a saki jagoran ‘yan Shi’a Ibrahim Elzakzaky ke cika.
Jostis Gebriel Kolawole wanda ya yanke hukuncin ya bukaci a ginawa Elzakzaky gida a duk inda ya ke bukata a jihar Kaduna.
Zuwa rubuta wannan labarin ba labarin daukaka kara daga jami’an tsaron Nijeriya kan hukuncin na babbar kotun ko kuma yiwuwar sake shi.
Tuni dai kungiyar ‘yan Shi’an ta sanarwa daga kakakin su Ibrahim Musa suka ce sun bankado wata kullalliya ta jefa fitina a kungiyar da za ta hana sake Elzakzakin.
Kungiyar dai ba ta fadi abun da ta dogara da shi wajen wannan ikirarin ba sai anbatar wata boyayyiyar majiya da ta ce ta na daf da hukumomin tsaro.
Gwamnatin jihar Kaduna dai ta haramta aiyukan muzahara da tare hanya na kungiyar ta Elzakzaky inda ta bukaci jami’an tsaro su ci gaba da zuba ido kan ‘yan kungiyar da ta zarga da tada fitina da raina kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Wani jagoran al’ummar Gyellesu Zaria inda a da gidan Elzakzaky ya ke gabanin rushe gidan ya nuna rashin amincewa da hukuncin babbar kotun Najeriya da bukatar Jostis Kolawole ya nemawa Elzakzaky gida a garin su amma ba Gyellesu ba.
Sakataren na kungiyar raya Gyellesu Mallam Muntari Gambo a zantawa da JARIDAR DAILY TRUST ta ranar 17 ga Disamba 2016 ya ce almajiran Elzakzaky sun gallaza mu su azaba da ma sanadiyyar mutuwar mutane a yankin har ma da jefa rayuwar masu juna biyu cikin gararin mutuwa.