‘Wa’adin daina amfani da tsohon kuɗi bai ƙare ba’Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile

Asalin hoton, GODWIN EMEFIELE/TWITTER

Bayanan hoto,

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile

Babban bankin Najeriya ya tabbatar wa BBC cewa har yanzu ba a daina amfani da tsofaffin kuɗi ba a faɗin ƙasar.

Wani babban jami’i a CBN ya shaida wa BBC cewa bisa la’akari da umurnin da kotun ƙolin Najeriya ta bayar na a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin har zuwa ranar 15 ga watan Fabarairu, a domin haka CBN zai bi wannan umurnin har zuwa ranar da za a koma zama a kotun.

Jami’in ya ce a hukumance CBN bai fitar da wata sanarwa ba a kan wannan batun, amma dai bankunan kasuwanci a faɗin Najeriya ba za su daina karɓar tsofaffin kudi ba har sai bayan wa’adin da kotun kolin kasar ta bayar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta ce za ta mutunta umarnin da Kotun Kolin kasar ta bayar a kan karar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar inda kotun ta dakatar da aiwatar da wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi na naira 200 da 500 da kuma 1,000.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like