Wa’adin Ranar 31 Ga Wata Na Daina Amfani Da Tsoffin Kudaden Naira Na Nan Daram- CBN
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya a game da shirin daina amfani da tsoffin takardun kudin Naira a ranar 31 ga watan nan na Janairun da muke bankwana da shi sakamakon yadda ya dauki matakan bai wa bankunan hada-hadar kudi umarnin su rika aiki a ranakun Asabar don a iya cimma wannan burin.

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da kansa ya jadada cewa babu gudu ba ja da baya a game da wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudin Naira domin a fara amfani da sabbin takardun kudin da ake sauya fasalinsu.

Bankin CBN, ta bakin Emefiele, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar bankin dake Birnin Tarayya Abuja don sanar ‘yan kasa matsayar da kwamitin manufofin kudin kasar wato MPC ya cimma bayan taronsa na yini biyu da aka karkare a yau Talata 24 ga watan Janairun da muke ciki.

Mal. Haruna Bala Mustapha, shi ne daraktar sashin lura da sha’anin sanya ido a ayyukan bankuna na CBN, ya ce bankin ya yi hobbasa wajen tura ma’aikatansa zuwa dukannin jihohin kasar la’akari da korafe-korafen da yan kasa ke yi na rashin wadatuwar sabbin takardun kudin don cimma nasara a wa’adin da aka sanya.

A wani bangare kuma, mamba a kwamitin manufofin kudi da tattalin arzikin Babban Bankin CBN, Mal. Aliyu Rafindadi Sanusi, ya yi bayani a kan dalilan da ya sa zasu ci gaba da daga kudin ruwa don daidaita matsalar hauhawar farashin kayayyaki ga yan kasa don samar da sauki.

Tun bayan sanar da wannan mataki na janye tsoffin takardın kudin, babban bankin ya ce ya sanya matakai a dukkan sassan kasar don cimma aikin aiwatarwa ta hanyar tura ma’aikatan bankin da na bankunan hada-hadar kudi, baya ga tsare-tsaren kungiyoyin da ke amfani da POS da sauran fannonin hada-hadar kudi.

A game da harajin stamp duty da aka karba daga shekarar 2016 zuwa yau CBN ya ce an karbi tsabar kudi na naira biliyan 378 da miliyan 686 da dubu 315 da naira 505 da kwabo 28 ya zuwa yau sabanın alkaluma dake ta yaduwa bayan da Honarabul Gudaji Kazaure ya fito da maganar stamp duty.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdurra’uf:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like