
Asalin hoton, Getty Images
Tina Turner ta rasu ne a ranar Laraba tana da shekara 83
An haifi Tina Turner a jihar Tennessee ta ƙasar Amurka, kuma ta fara yin fice ne a lokacin da take cikin ƴan amshi a ƙungiyar mawaƙa da mijinta ke jagoranta, wadda ake kira `the kings of rhythm`.
Ba da daɗewa ba ta samu zama ɗaya daga cikin mawaƙa na ƙungiyar mijin nata, kuma sun fara samun kudi a harkar ne da wata waƙa mai taken `fool in love, da kuma `it`s gonna work out fine`.
Wasu fitattun waƙoƙin da suka yi tare a wancan lokacin su ne “1973`s Nutbush City Limits “River Deep – Mountain High”, “Proud Mary”, kafin kowa ya kama gaban sa.
Mijin ta shi ne wanda ya canza mata suna daga sunanta na haihuwarta, Anne Mae Bullock, zuwa Tina Turner, shawarar da ya ɗauka ba tare da saninta ba, wanda shi ne misali ɗaya na halayensa na cin zarafi da kuma nuna iko.
Asalin hoton, Getty Images
Tina Turner da mijinta Ike Turner
Ta tuna irin rauni da wahalar da ta sha a tsawon dangantakarsu da mijinta a cikin tarihinta na 2018, “My love story”.
Bayan kuɓutar ta daga mijin nata, ta ci gaba da gina sana`arta wadda ta sa ta zama daya daga cikin taurarin pop and rock na shekarun 1980 da 1990 da waƙoki kamar “Let`s stay together”, “Steamy windows”, “Private dancer”, sautin fim ɗin James bond golden eye”, da “I don`t wanna fight:, da kuma “It takes two”, da sukayi tare da Rod Sewart.
Ta samu farin ciki tare da mijinta na biyu, shugaban mawaƙan `Jamus, Erwin Bac, sun fara soyayya a tsakiyar shekarun 1980 kuma suka yi aure a shekarar 2013.
Ma`auratan sun zauna a Switzerland, a shekarar 2017, Erwin ya ba ta ƙodarsa ɗaya bayan da aka gano tana fama da ciwon ƙoda.
Ta shiga cikin mummunar hali lokacin da babban ɗanta ya kashe kansa a cikin shekarar 2018.
Wani yaron nata kuma, wanda baban sa shi ne Ike Turner ya mutu a cikin shekarar 2022.
Asalin hoton, Getty Images
Tina Turner da Ike Turner lokacin da suka yi waƙa a Birtaniya