Wadanda Su Ka Tsallake Rijiya A Tawagar ‘Yan Tijjaniyya A Kisan Burkina Faso Sun Isa Kaulaha
Mutanen wadanda ke tafiya a motoci daban-daban sun fito ne daga jihohin arewacin Najeriya daban-daban inda akasin ya yi sanadiyyar rasa ran mutum 15.

In za a tuna kungiyar ‘yan Tijjaniyya ta Ansarul Din Attijjaniyya ta baiyana cewa haka kurum jami’an soja su ka tare matafiyan su ka zabi wadanda su ke son kashewa inda su ka bindige wasu daga cikin su.

Ma’aikatar wajen Najeriya ta bakin ministan waje Ambasada Zubairu Dada ta yi alwashin binciken abun da ya faru don bin hakkin wadanda su ka rasa ran su.

“Zabe wadanda su ke son kashewa su ka yi inda wasu suka harbe wasu sannan wasu suka ce su ruga da gudu sai su ka harbe su” Inji Baba Shehu da ke cikin tawagar.

Shi kuma Abubakar Aliyu ya ce a motar su shi kadai a ka bari ba a sauko da shi inda ya cigaba da addu’a kuma a ganin idon sa a ka budewa mutane wuta jini ya yi ta zuba.

Saurari rahoton:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like