Kungiyar manyan ma’aikatan mai da iskar gas a Najeriya PENGASSAN ta fara wani yajin aiki a kasa baki daya.
Yajin aikin kungiyar na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake tsaka da fuskantar karancin man fetur a duk kanin fadin ƙasar.
Ibe Kachikwu karamin ministan mai na Najeriya ya alakanta ƙarancin man da ake samu kan raguwa da aka samu wajen samar da man da ake buƙata inda yace za a kawo karshen layukan man cikin yan kwanaki kaɗan masu zuwa.
A wata sanarwa cikin makon da ya gabata PENGASSAN ta bawa kamfanin Neconde Energy wa’adin awanni 72 da ya dawo da ma’aikatan da ya kora bakin aikinsu.
Yinkurin Kachikwu na shiga tsakani ya ci tura inda hakan ya janyo kungiyar ta tsunduma yajin aiki a ranar Litinin.
Chris Ngige, ministan kwadago shima ya roki kungiyar kan ta janye shirin da take yi na fara yajin aikin domin kare yan Najeriya daga fuskantar wahalhalu a yayin bukukuwan Kirsimeti da kuma na sabuwar shekara.