BBC ta yi waiwaye kan irin abubuwan da suka wakana tsakanin 1 zuwa 8 ga watan Afrilu ciki har da mutuwar mai ɗakin gwamnan Kano na farko da ɗage muƙabala da Sheikh Idris ‘kan zargin munana kalamai.
NAHCON ta sanar da kuɗin kujerar hajjin bana
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON, ta sanar cewa maniyyata aikin hajjin bana za su biya kuɗi da ya kai naira miliyan biyu da dubu 890 a matsayin kuɗin kujera.
Shugaban hukumar Zikrullah Hassan, shi ya bayyan haka ranar Juma’a, inda ya ce matsalar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da kuma Saudiyya a matsayin abubuwan da suka janyo ƙaruwar kuɗin hajjin bana.
Hassan ya ce farashin ya kai matakai takwas, inda jihohin Borno da Yobe suka kasance jihohi da za su biya kuɗi mafi ƙanƙanta yayin da Legas da Ogun za su biya kuɗi mafi girma da ya kai naira miliyan biyu da dubu 990.
Hakan ya faru ne sakamakon bambancin kuɗin jirgi da kuma kuɗin masaukai a Makka.
Maniyyatan jihohin arewacin ƙasar za su biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da goma sha tara.
Jihohin kudancin kasar kuma su ma za su biya kusan miliyan uku.
Ɗage muƙabala da Sheikh Idris ‘kan zargin munana kalamai
Asalin hoton, FACEBOOK/DUTSEN TANSHI MASJID BAUCHI
Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi ta yi ƙarin haske a kan dalilanta na ɗage zaman tattaunawa da ta shirya da Sheikh Idris Abdul’aziz, wanda ake zargi da munana kalamai a kan Annabi Muhammadu.
Tun farko ranar Asabar ne, hukumar ta shirya gudanar da muhawara da malamin addinin Musuluncin, sai dai sa’o’i kafin lokacin sai ga wata sanarwa da ke cewa an ɗage zaman.
Ana zargin fitaccen malamin ne da furta kalamin cewa ‘ba ya buƙatar taimakon Annabi’, abin mafi yawan mutane ke gani, munana lafazi ne ga Fiyayyen Halitta.
Lamarin ya janyo muhawara mai zafi da ka-ce-na-ce har a tsakanin malaman addinin Musulunci da ke arewacin Najeriya, inda wasu suka fara kiraye-kirayen lallai hukumomi su ɗauki mataki.
Mustafa Baba Illelah, shugaban Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi ya ce abin da ya sa suka ɗage zaman shi ne a bayar da dama ga malamin, da kuma sauran malaman da za su yi muhawarar, har ma da hukumomi duk su shirya.
‘Tinubu ne zai yanke shawara kan cire tallafin man fetur’
Asalin hoton, FACEBOOK/BOLA TINUBU
Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ne aka bar wa wuƙa da nama don ya yanke shawara game da lokacin cire tallafin man fetur a ƙasar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar mai jiran gado, Abdul’aziz Abdul’aziz ne ya tabbatar da haka a wata hira da BBC Hausa.
Ya ce wannan mataki ne da gwamnatin Najeriya take ɗauka a yanzu saboda wa’adin mulkinta ya kusa zuwa ƙarshe. “Yau, ƙasa da kwana sittin,” ke nan ta miƙa mulki.
Gwamnatin Najeriya ƙarƙashin Shugaba Buhari mai barin gado ta faɗa a watan Janairu cewa a cikin wannan wata na Afrilu ne za a fara cire tallafin man fetur.
Ministar kuɗin ƙasar, Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana haka a cikin watan Janairu, yayin wani taron tattalin arziƙi a Switzerland.
Ban taɓa sa ƙabilanci ko addini a yaƙin neman zaɓe ba – Peter Obi
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen da ya wuce, Peter Obi ya ce da alama ministan yaɗa labaran Najeriya, Lai muhammad yana son rataya masa jakar tsaba.
Ya ce ministan yana wannan yunƙuri ne game da wata tattaunawar wayar salula tsakanin Obi da Bishop David Oyedepo, wani babban limamin Kirista na majami’ar Living Faith Church, wadda ta janyo muhawara mai zafi da ce-ce-ku-ce.
Wannan ne karon farko da Peter Obi ya fito ya maida martani game da lamarin, tun bayan kwarmata tattaunawar. Ya wallafa martanin ne a shafinsa na Tuwita.
Shi dai Mista Lai Mohammed ya zargi Peter Obi da cin amanar ƙasa, kasancewar a tattaunawar an ji yadda ɗan takarar yake alaƙanta siyasarsa, tamkar wani yaƙi na addini tare da tabbatar wa limamin kirista cewa, (Kiristoci) ba za su yi da na sanin goya masa baya ba.
Peter Obi ya ce abin takaici ne yadda ake ta yunƙurin ɓata masa suna da kuma kasancewar hakan na zuwa ne daga wajen ministan gwamnati.
A cewar Peter Obi, bai taɓa yin wata magana ko kuma ƙarfafa gwiwar a yi wa Najeriya maƙarƙashiya ba sannan ya ce bai taɓa ɗaukar nauyi, ko ma furta wani mummunan abu game da Najeriya ba.
Mutuwar Uwargidan gwamnan Kano na farko
Asalin hoton, Other
A ranar Laraba ne, aka yi jana’izar uwargidan tsohon gwamnan Kano, Hajiya Ladi Baƙo, bayan ta rasu a wani asibiti da ke jihar.
An sallaci gawar marigayiyar mai shekara 93 a fadar Sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu salla, kafin a binne ta daga bisani.
‘Yar marigayiyar, kuma tsohuwar kwamishiniya a jihar Kano, Hajiya Zainab Audu Baƙo ce ta tabbatar da mutuwar cikin alhani lokacin zantawa da BBC Hausa ta wayar tarho.
Mijin marigayiyar, Kwamishinan ‘Yan sanda, Audu Baƙo ya jagoranci Kano a matsayin gwamna daga 1967 zuwa 1975.
Ya shahara a matsayin ɗaya daga cikin gwamnonin Kano da suka fi aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa a jihar.
Obasanjo ya nemi kotun Birtaniya ta sassauta wa Ekweremadu
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya rubuta wa jami’an kotu a Birtaniya, inda yake bukatar a yi sassauci lokacin yanke wa sanatan Najeriya Ike Ekweremadu da matarsa hukunci bayan kama su da laifin ‘safarar sassan jikin ɗan bil’adama.’
A watan da ya gabata ne kotu ta samu sanata Ike Ekweremadu mai shekara 60 da matarsa Beatrice da kuma wani likita Dr Obinna Obeta da laifin ɗaukar wani matashi ɗan shekara 21 daga Legas zuwa Birtaniya domin cire ƙodarsa, domin a bai wa ƴarsa Ekweremadu, mai suna Sonia, mai shekara 25.
A wasikar da Obasanjo ya rubuta, ya ce abin da ma’auratan suka yi ba daidai ba ne kuma babu wata al’umma da za ta lamunci aikata hakan.
Sai dai ya bukaci kotun da ta duba lamarin ƴar sanatan wadda lafiyarta ke cikin haɗari da kuma ke son agajin lafiya na gaggawa domin sassauta masa.
Obasanjo ya kuma faɗa wa kotun cewa ta duba ɗabi’u masu kyau da Ekweremadu ke da su a lokacin yanke masa hukunci.