Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata
Nan da kwana bakwai za mu magance matsalar kuɗi – Buhari
Asalin hoton, @Buhari Sallau
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci ƴan ƙasar da su ba shi kwanaki bakwai kacal domin shawo kan matsalolin kuɗi da suke kawai tasgaro a ƙasar.
Shugaban ya bayyana haka ne a wani taro da ya yi da ƙungiyar gwamnonin Jam’iyyar APC waɗanda suka je fadar shugaban ƙasar domin neman mafita kan ƙarancin kuɗin da ake fama da shi waɗanda suka ce hakan na barazana kan ayyukan alkhairi da gwamnatin ta yi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaban ya ce sauya fasalin kuɗin da aka yi zai haɓaka tattalin arzikin ƙasar da kuma samar da tagomashi na tsawon lokaci ga ƙasar.
Asalin hoton, KADUNA GOV FB
A cikin makon da ya gabata ne Gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna, ya yi wasu kalamai da suka janyo c-ce-ku-ce, inda ya ce a matsayinsu na gwamnonin arewa za su yi iyakar ƙoƙari wajen ganin mulkin Najeriya, ya koma hannun mutanen kudu a zaɓe mai zuwa.
Cikin wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, El-Rufai, ya ce “Duk wani zagon ƙasan da ake yi insha Allahu zaɓen nan mun riga mun ci shi, kuma ba ja da baya za mu yi wannan yaƙi, za mu kuma kunyatasu mu nuna musu cewa mu ‘yan Arewa ba mutanen banza bane”.
Gwamnan na Kaduna ya ce, “Batun wani dattawa, ba wani dattawa, ni ma dattijo ne domin a wannan shekarar ta 2023 zan cika shekara 63, don haka su waye dattawan Arewa, mu gwamnonin Arewa mu ne dattawan Arewa kuma mune shugabannin Arewa.”
Abin da ke faruwa a APC kan yaƙin neman zaɓen Tinubu
Asalin hoton, Getty Images
Tun gabanin zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ne ake raɗe-raɗin cewa akwai ɓaraka a jam’iyyar game da wanda zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa, musamman ma wanda shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ke mara wa baya.
Sai dai duk da nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu na kasancewa ɗan takara, lamarin bai mutu ba.
Wasu kalamai da ke fitowa daga bakunan makusantan Bola Tinubu, da shi kansa, da kuma ɓangaren makusantan shugaba Muhammadu Buhari na haifar da tababa kan alaƙar muhimman ɓangarorin biyu da ke da matuƙar tasiri kan nasarar jam’iyyar a babban zaɓen Najeriya na 2023.
An lalata kayayyakin zaɓe a hari kan ofishinmu – INEC
Asalin hoton, Getty Images
A makon da muke ban kwana da shi ɗin ne kuma wasu mahara suka kai hari kan ofishin hukumar zaɓen Najeriya a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin ƙasar.
A wata sanarwar da kwamishinan hukumar, kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a na hukumar Fetus Okoye ya fitar ya ce harin ya lalata ginin hukumar tare da kujerun da ke cikin ofishin.
Haka kuma harin ya yi sanadin lalata wasu kayyakin zaɓen waɗanda suka haɗar da akwatunan zaɓe 729 da kewayen da ake kaɗa ƙuri’a a ciki 243, da jakankunan zaɓe 256, da manyan wayoyi 11 da sauran kayayyakin zaɓe waɗanda aka riga aka kai su ofishin a shirye-shiryen gudanar da zaɓen ƙasar da ke tafe.
Rasuwar Dutse Nuhu Muhammad Sunusi
Asalin hoton, MUMINPHOTOGRAPHY
Haka kuma a cikin makon da muke ban kwana da shi ɗin ne Allah ya yi wa Sarkin Dutse, Nuhu Muhammad Sunusi rasuwa.
Kwamishinan ayyuka na musamman a Jihar Jigawa Auwal Danladi Sankara ne ya tabbatar wa BBC da rasuwar sarkin ranar Talata da yamma.
Sarkin ya rasu ne a wani asibiti a Abuja bayan ya yi fama da gajeren rashin lafiya kuma ya rasu yana da shekara 79.
A ranar Laraba ne aka yi jana’izar sarkin a fadarsa da ke Dusten jihar Jigawa
Jana’izar sarkin ta samu halartar manyan daga ko’ina a faɗin ƙasar, ciki har da sarakuna da manyan jami’an gwamnati da masu riƙe da muƙamai da ‘yan siyasa.