
Naɗa kwamitin miƙa mulki
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin kwamitin shirye-shiryen mika mulki na ofishin shugaban kasa, wanda zai gabatar da dukkan ayyukan shirin mika mulki ga sabuwar gwamnatin da za ta gaji wannan bayan zaben 2023.
Wannan na cikin wata sanarwa da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar da sa hannun Willie Bassey wanda shi ne daraktan yada labarai a ofishin.
1. Sakataren Gwamantin Tarayya – Shugaban kwamitin 2. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya 3. Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma babban sakatare a ma’aikatar shari’a
Bai wa INEC kuɗaɗen gudanar da zabukan 2023
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta sanar cewa gwamnatin kasar ta mika mata dukkan kudaden da ta ke bukata domin gudanar da babban zabe na kasar na 2023 wanda za a yi a karshen wannan watan.
Hukumar ta kwantar wa ‘yan kasar hankula kan rahotannin da ke yawo cewa tana fuskantar matsalolin kudi. Sakataren hukumar na gudanarwa na jihar Kaduna,
Auwal Mashi ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki da kuma horar da ‘yan jarida kan amfani da sabon tsarin tantance masu zabe mai suna Bimodal Voter Accreditation System (BVAS).
Ya kuma ce dukkan kayayyaki masu muhimmanci na hukumar tuni aka kai su dakin ajiyar babban banki Najeriyar.
“Mun dauki ma’aikata 34,000 domin gudanar da zabukan a jihar Kaduna, domin su yi aiki a rumfunan zabe 8,012 na jihar.
Nasarar sojojin Najeriya ta kashe ‘yan bindiga 77
Asalin hoton, NDF
Ma’aikatar tsaro ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa da ke cewa dakarun kasar sun kashe barayin daji 77 yayin samamen da suka kai a sassan arewacin kasar, musamman a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya.
Sanarwar wadda ta fito daga hannun Manjo-Janar Musa Danmadami, wanda shi ne babban jami’i mai kula da harkoki yada labarai, ta ce cikin makonni biyun da suka gabata sojojin Najeriya suka sami wadannan nasarorin.
Manjo-Janar din yi wannan bayanin ne a Abuja – yayin ganawa da manema labarai da ma’aikatar tsaro ta saba yi da manema labarai sau biyu a kowane mako kan ayyukan rundunonin sojojin Najeriya.
A misali, Janar Danmadami ya ce dakarun da ke aikin tabbatar da tsaro na Operation Hadin Kai a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram da na ISWAP guda 56, sannan sun kama mayaka 26 baya ga ceto da 59 da suka yi.
Ƙarar da gwamnatin jihar Kano ta kai gwamnatin Buhari
Asalin hoton, KSG
Gwamnatin Jihar kano ta kai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kara a gaban Kotun Kolin kasar a kan sauyin fasalin wasu daga cikin manyan kudin kasar na naira 200 da 500 da 1,000.
A karar wadda Babban Lauyan jihar ta Kano ya shigar ta hannun Sunusi Musa babban lauya a Najeriya (SAN), a jiya Alhamis, gwamnatin tana bukatar kotun ta ayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari shi kadai ba shi da hurumin umartar Babban Bankin Kasar, CBN ya dakatar da amfani da takardun kudin na naira 200 da 500 da kuma 1,000 ba tare da tuntuba da amincewar majalisar tattalin arziki da kuma majalisar zartarwa ta kasar ba.
A don haka ne gwamnatin jihar ta Kano take son Kotun ta soke matakin Babban Bankin na Najeriya na janye takardun kudaden saboda abin ta kira wahalar da al’ummar jihar ke ciki asaboda matakin na CBN.
A tattaunawarsa da BBC lauyan da ya shigar da karar Sunusi Musa ya ce a ranar Laraba ne Kotun za ta saurari karar.
Matsayar Majalisar Magabatan Najeriya kan sauyin kuɗi
Asalin hoton, BA
Majalisar magabata ta kasa a Najeriya wato Council of State, ta kammala wani taron gaggawa a fadar shugaban kasar da ke Abuja inda ta bukaci babban bankin kasar, CBN ya samar da karin sababbin takardun kudi domin amfanin al’ummar kasar.
A cewar majalisar, idan sababbin kudin ba za su samu ba, to CBN ya koma bai wa jama’a tsofafun takardun kudin.
Majalisar – wadda ke karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari – ta kira taron ne domin tattaunawa ka halin da kasar ke ciki a yanzu da ta ke tunkarar babban zabe.
Majalisar ta kunshi tsofaffin shugabannin Najeriya da shugabannin majalisar dattawa da na wakilai da wasu ministoci da kuma gwamnonin kasar.
Ta kuma ce duk da matsalolin da ake fuskanta, tana goyon bayan tsarin babban bankin na sake fasalin naira.