Wannan maƙala ce da ke duba muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata
CBN ya ƙara yawan kuɗin da za a dinga cirewa daga banki
Asalin hoton, CBN
Babban bankin Najeriya CBN, ya yi amai ya lashe kan matakinsa na ƙayyade yawan kuɗaɗen da za a dinga cirewa daga bankuna a ƙasar.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, CBN ya ce a yanzu ɗaiɗaikun mutane za su iya cire kuɗi har naira 500,000 yayin da kamfanoni kuma za su iya cire naira miliyan biyar duk mako.
Wannan sabon matakin na CBN na zuwa ne kwana 15 bayan fitar da dokar farko da ta ƙayyade yawan kuɗaden da mutane za su iya cirewa daga bankunan a duk sati.
Majalisar dattawan Najeriya ta ƙi amincewa da kasafin kuɗin 2023
Majalisar dattawan Najeriya ta ƙi amince wa da kasafin kuɗin ƙasar na 2023 da ta shirya amince wa da shi a yayin zaman majalisar na ranar Alhamis ɗin da ta gabata.
Shugaban Majalisar dattijan ƙasar Ahmad Lawan ya ce rashin amincewa da kasfain kuɗin ya biyo bayan kura-kurai ne da kasafin kuɗin ke ƙunshe da shi, daga ɓangaren gwamanti.
“Sakamakon wasu ƙalubale, ba za mu iya karɓar rahotan kwamitin kula da kasafin kuɗin ƙasar ba saboda, ya zo majalisa da matsaloli”.
Kotu ta ce Muhammad Abacha ne dan takarar gwamnan Kano a PDP
Asalin hoton, FACEBOOK/MUHAMMED ABACHA
Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke hukuncin cewa Muhammad Abacha ne ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Mai Shari’a AM Liman ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis ta manhajar Zoom kasancewar baya gari.
An dai samu rarrabuwar kawuna a lokacin gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar a jihar, lamarin da ya sa aka samu ɓangarori biyu waɗanda ke ikirarin yin halastaccen zaɓen fitar da gwani
Saudiyya ta bai wa Najeriya kujeru 95,000 a Hajjin 2023
Asalin hoton, NAHCON
Saudiya ta dawo wa da Najeriya adadin kujerun da ta saba ba ta sama da 95, 000, na mutanen da za su je aikin Hajji a 2023.
Hukumar ƙasar ta Saudiya ta bayyana hakan ne a wata ganawa da hukumar alhazan Najeriya, a ranar Laraba.
Suwaiba Ahmad, mai magana da yawun hukumar alhazan Najeriya ce ta tabbatar wa BBC matakin na Saudiya.
Shugaba Buhari ya yi alƙawarin inganta rayuwar ‘yan sandan Najeriya
Asalin hoton, STATEHOUSE
Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da aniyar gwamnatinsa ta inganta aiki da rayuwar ‘yan sandan Najeriya.
Sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a makon da ya gabata, lokacin da ya karɓi rahoto kan rundunar ‘yan sandan ƙasar na shekarar 2021, da karɓar ƙudurin kasafin kuɗin ‘yan sanda na baɗi.
Sanarwar ta ambato shugaba Buhari na cewa: “wannan gwamnatin ta sanya walwala da inganta aikin ‘yan sanda a sahun gaba, kuma hakkinta ne ta kawo sauye-sauye masu inganci a aikinsu.