
Asalin hoton, CBN
Babban bankin Najeriya CBN ya ce ba gudu ba ja da baya game da wa’adin da ya sanya na daina amfanin da tsoffin takardun kuɗin ƙasar daga ranar 31 ga watan Janairu.
Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka cikin makon da ya gabata, bayan ganawar kwamitin babban bankin kan tsare-tsaren kuɗi.
Mista Emefiele ya jaddada cewa babban bankin ya bayar da wadataccen lokaci ga ƴan ƙasar da su mayar da tsoffin kuɗadensu zuwa bankunan ƙasar domin musanya su da sabbi.
Ya ƙara da cewa kawo yanzu babban bankin ya karɓi tsoffin takardun kuɗi da adadinsu ya kusa naira tiriliyan 1.5, tare da fatan cewa za su iya kai wa tiriliyan biyu kafin cikar wa’adin da bankin ya saka.
Majalisar wakilai ta umurci a kai gwamnan CBN gabanta ranar Talata
Majalisar ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta gayyaci gwamnan babban bankin har sau biyu ba ya zuwa.
Wani rahoto na cewa ‘yan majalisar suna so ne su ji daga bakin gwamnan dalilin da ya sa ba za a ƙara wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun naira ba.
Waɗanda bankin ya ce za su daina aiki daga ranar 31 ga wannan wata na Janairu.
‘Bam ya kashe Fulani 27 a jihar Nasarawa’
Asalin hoton, Getty Images
Jami’an tsaro a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar aƙalla Fulani 27, yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon tashin bam a wani ƙauye da ke kan iyakar jihohin Nasarawa da Benue.
A tattaunawarsa da BBC, kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa Maiyaki Muhammed Baba, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce sun samu labarin faruwar al’amarin ne da safiyar ranar Laraba.
Ya ce “mun tashi da safen nan aka ce mana an jefa bam, ko kuma wani bam ya tashi, akwai gawarwaki da yawa da shanu waɗanda aka yi asara”.
Ya ƙara da cewa yanzu da haka hukumar ƴan sanda na ci gaba da bincike kan lamarin.
Ana yi wa zaɓen 2023 zagon ƙasa – Tinubu
Asalin hoton, Tinubu /Facebook
Dan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin cewar da gangan aka ƙirƙiri batun sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar da batun ƙarancin man fetur domin hana gudanar da zaɓen ƙasar da ke tafe.
Mista Tinubu ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar cikin makon da ya gabata.
“Ba sa so zaɓen ya gudana. Suna buƙatar hana gudanar da shi. Shin za ku bar su?”, in ji Tinubu a lokacin da yake tambayar dubban magoya bayansa da suka halarci taron gangamin a filin wasa na MKO Abiola a birnin Abeokuta.
Hisbah ta fara binciken matar da ta auri saurayin ƴarta a Kano
Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma a cikin makon da muke bankwana da shi ɗin ne kuma ana samu ɓullar labarin wata mata da ake zargi da aurar saurayin ‘yarta a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Labarin ya soma ɓulla ne bayan da iyayen matar suka zargi shugaban Hisba na ƙaramar hukumar Rano da aurar ta ‘yar tasu ba tare da izininsu ba.
Babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano da ke Najeriya Sheikh Harun Ibn Sina ya shaida wa BBC cewa ya kafa kwamiti domin gudanar da bincike game da zargin da ake yi wa wata matar na kashe aurenta tare da auren saurayin ƴarta.
“Kwanaki biyu da suka gabata ne labari ya iso teburina cewa wata mata ta kashe aurenta, inda kuma ta auri saurayin ƴarta, saboda haka nan take na kafa kwamiti domin yin bincike game da batun”.