Waiwaye: INEC ta fara raba katin zabe, kotu ta yanke wa Sheikh Abduljabbar hukuncin kisa
Kamar kowanne mako, wannan makalar na dauke da wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata.
Yadda aka fara raba katin zabe a Najeriya

Hukumar zaɓe a Najeriya, Inec, ta fara raba wa ‘yan ƙasar katinan kaɗa ƙuri’a a babban zaɓe na 2023.
An fara raba katinan ne a ofisoshin Inec na kananan hukumomi da ke faɗin ƙasar, inda ake raba katin mazaba-mazaba.
Duk mutumin da ya zo karbar katin sai ya gabatar da shaidar cewa ya yi rijista a baya sannan sai a duba sunansa a kundin rijistar zaɓe sai kuma a duba masa katin.
Idan an sami katin sai kuma a rubuta sunansa ya saka hannu cewa ya karbar.
Amma da farko sai mutum ya duba sunansa a kundin rijistar da aka yi baja-kolinta a jikin bango.
Wadanda ba su ga sunayensu ba a kan ba su wata takarda su cike sannan sai a bukaci su dawo daga baya don karbar katinsu. Za a shafe kwanaki ana wannan aiki na raba katunan zabe a matakin ƙaramar hukuma kafin a koma matakin mazabu.
‘Yan bangar siyasa sun kona ofishin PDP a Gombe
Jamiyyar PDP mai hammaya a jihar Gombe ta ce wasu da ake zargim yan bangar siyasa sun cina wuta a ofishin yakin neman zaben dan takararta na gwamnan jihar Mohamed Barde da tsakar daren jiya Litinin.
PDP ta kuma ce wannan ba shi ne karon farko da ake kai wa ofishinta hari ba.
Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta ce ta soma gudanar da bincike a kan lamarin.
Babu dai cikakkun bayanai kan harin, amma dai PDP ta zargi APC da wannan hari.
A sanarwar da ta fitar, Mohammed Barde ya ce sun tafka asara sosai a harin.
Sai dai babban jami’in yada labaran gwamna mai ci Inuwa Yahaya, ya ce PDP kawai na neman abin tallata kansu ne.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce sun kaddamar da bincike kan lamarin.
Abin da sababbin dokokin korona na matafiya da aka sauya a Najeriya ke nufi
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta kawo karshen tilasta sanya takunkumi ga ma’aikata a tashar jiragen sama da kuma fasinjoji.
Mutanen da takunkumi ya kasancewa wajibi a yanzu su ne wadanda suka haura shekaru 60.
Matakin gwamnatin kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ta ce daga yanzu matafiya sun daina nuna sakamakon gwajin cutar korona idan sun isa ko kuma za su yi tafiya zuwa wata kasa.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar ta ce an ɗauki matakin ne bayan tabbatar da cewa a yanzu ba kasafai ake samun wadanda suka kamu da cutar ba a Najeriya dama sauran kasashen duniya.
Me ke kunshe cikin sabbin dokokin Koronar?
Kusan a yanzu gwamnatin Najeriya ta gamsu cewa ba a fiya samun wasu dauke da korona ba a kasar.
Kuma bincikenta ya tabbatar da cewa ko a wasu kasashen adadin masu kamuwa da cutar ya ragu matuka.
Don haka kwamitin da ke yaki da annobar korona da aka kafa ta janye ko sassauta dokokinta 19 da ya zama wajibi mafiya a cikin gida da kuma masu shigowa su mutunta.
Ƙa’idar cire kudin CBN ta raba kan majalisar dattawan Najeriya
Asalin hoton, SENATE FACEBOOK
Kan ƴan majalisar dattawan Najeriya ya rabu biyu kan batun sabbin ƙa’idojin da babban bankin ƙsar CBN, ya fitar na ƙayyade cire kuɗaɗe.
Hakan ya faru ne a yayin gabatar da rahoton kwamitin da ke lura da sha’anin banki na majalisar dattijan kan sabbin tsare-tsaren da ka’idojin CBN din.
Wasu mambobin majalisar sun nuna goyon bayan tsarin na CBN yayin da wasu kuma suka nuna ƙin amincewa da sabbin ƙa’idoji cire kuɗaɗen.
Shugaban kwamitin Sanata Uba Sani ne ya gabatar da wannan rahoto a zaman da majalisar ta yi na ranar Laraba.
Ƴan majalisar sun shafe tsawon sa’a’o’i suna tafka muhawara a kan batun.
Sanata Uba Sani ya gabatar da rahoton mai cike da rudani, wanda kuma ‘yan majalisar suka yi ta jayayya akai.
A karshe an buƙaci a bayar da lokaci domin sake nazari kan shawarwarin da majalisar ta bayar.
An fara amfani da sabbin takardun Naira a Najeriya
Asalin hoton, Reuters
A ranar Alhamis 15 ga watan Disamba, ne aka fara amfani da sabbin takardun kudi da aka sauya a karon farko cikin shekaru 20 a Najeriya.
Hukumomi a kasar sun ce sun dauki matakin sauya fasalin kudin ne domin magance matsalar tsaro, da samun damar mayar da garin kudi bankunan kasar.
Babban bankin Najeriya ya ce kashi 80 cikin 100 na kudin da ke hannun jama’a na wurin wasu tsirarun mutane.
CBN ya bukaci ‘yan Najeriya su gaggauta mayar da tsofaffin kudaden da suke hannunsu bankuna, domin a sauya musu da sabbin.
Ranar 31 ga watan Janairu ne wa’adin da hukumomi suka kayyade zai cika ga mutanen da aka bai wa umarnin mayar da tsofaffin kudin banki.
Yawancin ‘yan Najeriya na ganin ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan abubuwan da suka fi damun ‘yan kasa, kamar magance hauhawar farashin kayayyaki, maimakon sauya fasalin kudi.
Kotu ta yanke wa Sheikh Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara, hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.
An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis 15 ga watan Disamba, bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same shi da dukkan laifi huɗu da ake tuhumar sa da su.
Daga cikin tuhumar da ake yi masa akwai da zargin tayar da tarzoma a jihar Kano ta hanyar wa’azinsa.
Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari’a Sarki Yola ya ɗage zaman kotun don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin.
Bayan dan lokaci kuma sai aka koma zaman kotun tare da yanke hukuncin.
Sai dai kafin a tafi hutun, Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara ya yi magana ta karshe inda ya ce bai san lauyan da ke kare shi ba kuma ba ya neman afuwa saboda, a cewarsa, bai aikata laifi ba kuma ya nemi a gaggauta yanke masa hukunci.
Mai Shari’a Sarki Yola ya ce malamin yana da kwana 30 don ɗaukaka ƙara idan bai gamsu da hukuncin ba.
A ranar Juma’a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.
An gano cibiyar haɗa bama-bamai ta ‘IPOB’ a Ebonyi
Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta ce ta samu nasarar gano wata cibiyar harhaɗa bama-bamai, mallakar kungiyar IPOB ta ‘yan aware mafi girma a kudu maso gabashin Naijeriya.
Wannan dai ya zo bayan jami’an tsaro na rundunar hadin-guiwa ta samu sahihan bayanai game da cibiyar da ake hada bama-bamai domin tayar da zaune tsaye cikin al’umma.
Ta kashe da kuma kama wasu mambobin IPOB, yayin da wasu suka tsere da munanan raunuka.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi Chris Anyanwu wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce binciken ya biyo bayan wani samame da ‘yan sandan suka kai inda suka yi artabu da ‘yan kungiyar IPOB/ESN
Mutum biyu sun hallaka daga cikin ‘yan kungiyar ta aware ta IPOB tare da kama daya daga cikin kwamandojin a cibiyar haɗa bama-baman.
Tawagar hadin guiwa ta Sojoji da jami’an tsaro na farin kaya da ‘yan sanda, sun dira inda Kwamandan da ake zargi yake kitsa barna tare da gano manyan abubuwa na tashin hankali.
Abubuwan da aka gano sun haɗa da “Ababan fashewa 30 da na’urorin haɗawa da kwance bama-bamai da sauran na’urori da sinadaran hada bama-baman daban-daban da ake hada nakiyoyin.
Yadda EFCC ta ƙwato biliyoyin naira cikin shari’a 3,000 da ta yi nasara a 2022
Asalin hoton, EFCC
Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce ta yi nasara a ƙararraki 2,595 da ta gurfanar da mutane a gaban kotu cikin shekarar 2022.
Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta ce ta samu nasarorin ne mafiya yawa a tarihinta ya zuwa 23 ga watan Satumba.
Hukumar ta bayyana cikin mujallarta da ta fitar bugun Satumba, inda ta ce tana fatan sake samun wasu nasarorin kafin shekarar ta ƙare baki ɗaya.
“Waɗannan nasarori masu abin mamaki sun samu ne a daidai lokacin da yin nasara a kotunan Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba, ” a cewar Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa yana mai alƙanta nasarar da ƙoƙarin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a yaƙi da rashawa.
EFCC ta yi nasara a shari’o’in da wasu daga cikinsu sai da suka kai har Kotun Ƙoli da Kotun Ɗaukaka Ƙara, amma akasarinsu an fafata ne a manyan kotunan tarayya da ke faɗin Najeriya.
A ranar Alhamis Abdulrasheed Bawa ya ce hukumarsa ta ƙwato da kuma mayar wa gwamnati naira biliyan 36 a 2022, kuma biliyan 30 sun ƙwace su ne daga hannun tsohon Babban Akanta na Ƙasa Idris Ahmed – wanda ke fuskantar shari’a kan zargin wawure biliyan 109.
Dalilin da ya sa Indiya ta tasa keyar ‘yan Najeriya 196 zuwa gida
Asalin hoton, Getty Images
Kasar Indiya ta tasa keyar wasu ‘yan Najeriya kusan dari biyu da sauka hada da maza da mata da kananan yara zuwa gida, sakamakon rashin gamsuwa da yanayin zamansu a kasar ta Indiya.
A maraicen ranar Juma’a ne hukumomin Najeriya suka karbi wadannan mutane a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, wadanda hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar, wato NEMA, ta yi dawainiyar kwaso su daga Indiyar.
Bashir Idris Garga, babban jami’in kai dauki na hukumar ta NEMA, ya yi wa BBC karin bayani.”Akwai wasu ‘yan Najeriya da ke zaune a Indiya, wadanda hukumomin kasar ba su gamsu da zamansu ba, ko kuma sun zama musu damuwa a kasar. Wannan ne yasa suka bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta dawo da su gida.”Ya ce Najeriya ta dauki matakin kwaso ‘yan Najeriyan su 196 zuwa Abuja.”
Maza 152, sannan mata 44, ciki har da kananan yara biyar, kuma yawancinsu ba su wuce shekara biyar da haihuwa ba.”
Sai dai jami’in na NEMA ya tabbatar wa BBC cewa yawancin ‘yan Najeriyan ‘yan asalin jihohin kudancin Najeriya ne, amam akwai wasu kadan cikinsu daga yankin arewacin kasar.