Abubuwa da dama ne suka faru a Najeriya a makon da muke ban kwana da shi, ciki har da cika shekara ɗaya da harin jirgin ƙasan Kaduna da naɗa shugaban riko na ƙasa da PDP ta yi.
DSS ta tabbatar da maƙarƙashiyar kafa gwamnatin riƙon ƙwarya
Asalin hoton, DSS/Facebook
A makon da muke yi wa bankwana ne, Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS, ta ce ta shaida wasu jiga-jigai da ke kitsa wata maƙarƙashiya don kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a ƙasar.
Hukumar ta ce maƙarƙashiyar, wadda wasu ke izawa ba kawai aba ce da ta saɓa wa doka ba, wani ƙoƙarin masu jamhuru ne na kifar da tsarin mulkin Najeriya da kuma jefa ƙasar cikin wani rikici da za a iya kauce masa.
Ta ce tunanin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, abu ne da ba za a amince da shi ba, a tsarin dimokraɗiyya da kuma muradin zaman lafiyar al’ummar ƙasar.
A saƙon da ta wallafa a shafinta na Tuwita ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labaran hukumar, Peter Afunanya, DSS ta ce tun bayan zaɓukan ƙasar da aka kammala cikin kwanciyar hankali, ake ta raɗe-raɗin kafa gwamnatin riƙo.
Sai dai DSS ba ta fito kai tsaye ta ce ga ƴan siyasar da take zargi da shirya wannan maƙarƙashiya ba.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta yi aiki da sauran hukumomin tsaro don ganin an yi bikin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
PDP ta dakatar da Ayu, ta kuma naɗa shugaban riƙo na ƙasa
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne kotu a Binuwai ta haramta wa Dr Iyorchia Ayu ci gaba da gabatar da kansa a matsayin shugaban PDP, har sai ta saurari ƙarar da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka shigar gabanta.
Babbar jam’iyyar adawar ta Najeriya ta sanar da dakatar da Ayu, bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amana.
Bayan nan ne kuma Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDPn ya amince da naɗin Ambasada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ya ce sun ɗauki matakin naɗa Damagum ne domin bin umarnin tsarin mulkin PDP da kuma martaba umarnin kotun da ta yanke hukunci kan Ayu.
INEC ta tsayar da ranakun ƙarasa zaɓuka, zaɓaɓɓun gwamnoni sun karɓi shaidar cin zaɓe
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta sanya Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranar ƙarasa zaɓukan da ba su kammala ba a jihohi da dama na ƙasar.
Ta ce za ta ƙarasa zaɓukan da ba su kammala ba, na gwamna a jihohin Kebbi da Adamawa, sai na ‘yan majalisar dattijai guda 5, da na ‘yan majalisar wakilai 31, da kuma na ‘yan majalisun jihohi guda 58.
Za a gudanar da zaɓukan ‘yan majalisun dokokin ne in ji INEC a wasu cibiyoyin zaɓe ƙalilan na mazaɓun ɗan majalisa.
A ranar Litinin ne 27 ga watan Maris, hukumar zaɓe ta INEC ta yi wata ganawa don bitar wuraren da ake buƙatar ƙarasa zaɓukansu, saboda rashin kammalawa a lokacin zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya.
A ranar Laraba 29 ga watan Maris da kuma 31 ga watan Maris ne INEC ta bayar da takardar shaidar cin zaɓen ga zaɓaɓɓun gwamnoni da mataimakansu, tare kuma da ‘yan majalisun dokokin jihohi.
‘Ƙaddamar da rijiyar man fetur a jihar Nassarawa’
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙar rijiyar man fetur a ƙaramar hukumar Obi a jihar Nasarawa da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.
Ƙaddamar da aikin tona rijiyar zai sa kamfanin mai na ƙasar NNPC Ltd, ya fara tono man fetur daga jihar.
A cikin watan Nuwamban bara ne dai shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Yawancin man da ƙasar ke da shi dai tana haƙoshi ne daga yankin Niger Delta a kudu maso kudancin ƙasar.
Najeriya dai ta dogara ne kan man fetur da take fitarwa a matsayin hanayr samun kuɗin shiga, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnatocin ƙasar ke yi na faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga ga ƙasar.
Shekara ɗaya da harin jirgin ƙasan Kaduna
Asalin hoton, others
Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna a Najeriya ta ce shekara guda bayan kai harin jirgin ƙasa a jihar, har yanzu akwai kayayyakin fasinjojin jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka sace a ma’aikatar.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ma’aikatar ta ce bayan aukuwar harin a shekarar da ta gabata, ma’aikatar ta ɗauko jakankunan fasinjojin bayan da jami’anta suka hallara wurin da lamarin ya faru.
To sai dai a cewarta har yanzu akwai jakankuna 16 da ke hannunta, ba tare da an karɓe su ba.
A ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2022 ne dai wasu mahara suka tare jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, bayan da suka lalata hanyar jirgin da abin fashewa.
Sannan kuma suka sace fasinjoji masu yawa tare da yin garkuwa da su.
Fasinjojin dai sun kwashe kimanin watanni a hannun ‘yan bindigar, inda suka riƙa sako fasinjojin rukuni-rukuni.
Sun dai saki rukunin ƙarshe na fasinjojin da ya ƙunshin mutum 23 a farkon watan Oktoban 2022.
Gawuna ya taya Abba ‘Gida-Gida’ murnar cin zaɓe
Mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar, Nasir Yusuf Gawuna ya yi wa zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf addu’ar samun nasara a mulkinsa tare da yi wa kansa da magoya bayan jam’iyyar APC fatan ɗaukar kaddara.
Gawuna ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙon murya da aka naɗa, wadda mai taimaka masa kan harkar yaɗa labarai, Hassan Musa Fagge ya aiko wa BBC.
Matakin na zuwa ne jim kaɗan bayan Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta bai wa Abba Gida-Gida takardar shaidar cin zaɓen gwamna a ranar Larabar da ta gabata.
Gawuna ya buƙaci magoya bayansa su ƙara haƙuri tare da addu’ar ɗaukan ƙaddara a rashin nasarar da jam’iyyar ta yi a zaɓen gwamna na shekarar 2023.
A ranar 20 ga watan Mayu ne, INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano bayan zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan na Mayu.
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan Kano Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya ce Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.
Sai dai jam’iyyar APC ta ce ba ta yarda da sakamakon ba, kuma ta buƙaci INEC ta sake nazari kan zaɓen.