An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17-Disamba-1944, a garin Daura da ke cikin jihar Katsina, arewacin taryyar Nijeriya. Buhari ne da na 23 a cikin ‘ya’yan mahaifinsa Malam Adamu. Sannan ya tashi a hannun mahaifiyarsa mai suna Zulaihatu bayan rasuwar mahaifinsa yana dan shekaru hudu a duniya.
Banda karatun addini a gida, Buhari ya shiga makarantar firamari ta Daura da Mai’adua, sannan ya je Katsina Model School a shekara 1953, sai kuma Katsina Provincial Secondary School (wanda ake kira Government College Katsina a yanzu) daga 1956 zuwa 1961.
Daga nan ne ya shiga makarantar soje ta Nigerian Military Training College da dake kaduna , inda ya fara aikin soja.
Buhari ya ci gaba da karatu a ciki da wajen kasar, a makarantu wadanda suka hada da,:
Defence Services Staff College, Wellington, India, a shekara 1973. Sannan Army Mechanical Transport School a birnin Borden, na kasar Britania.
Karatunsa na karshe shi ne na The United States Army War College(USAWC) a Carlisle, na jihar Pennsylvania, a kasar Amurka inda ya sami digiri na biyu ko kuma Masters Degree a ilmin sanin dabarun yaki ko Strategic Studies.
Kafin ya zama shugaban kasa a karon farko a shekara 1983, Buhari ya rike wasu manya manyan mukaman gwamnati wadanda suka hada da gwamnan jihar Arewa Maso Gabas, da ministan man fetur da albarkatun kasa.
A shekara 1983 Buhari da abokansa cikin rundunar sojojin kasar suka yi juyin mulki wa zabebben gwamnatin Shehu Shagari bayan zarginta da lalata tattalin arzikin kasar sanadiyyar cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa.
A cikin gwamnatin da ya jagoranta na watannin 20, muhimman lamura da ya aiwatar a bangaren tattalin arziki shi ne canza launin kudaden kasar, don raya bankuna da kuma lalata shirin attajiran kasar wadanda suka bobboye kudade a wurere daban daban.
Har ila yau Buhari ya ki amincewa da bukatar Bankin lamuni ta duniya IMF na ya rage darajar Naira da kashi 60%, a maimakon haka ya takaita shigir da kayaki daga kasashen waje wadanda za su cutar da tattalin arzikin kasar da sauransu. A kokarin gyara halayen ‘yan Nigeria kuma, Buhari ya jefa ‘yan siyasa da dama cikin gidan kaso tare da tuhumar sata da cin hanci da rashawa, sannan ya gabatar da shirin yaki da rashin da’a da nufin kyautata halayen ‘yan Nijeriya.
Sai dai kamar yadda ake zata ya sha suka daga banagren kungiyoyi da kasashen duniya kan take hakkin bi’adama musamman ‘yan jaridu.
Bayan an yi wa gwamnatinsa juyin mulki a shekara 1985, gwamnatin Babangida ta tsare shi na wasu shekaru. Sai kuma bayan darewar marigayi Janar Sani Abacha kan kujerar shugabancin kasar ya kafa hukumar PTF wacce ta gudanar da ayyukansa da tarin kudaden man fetur da aka yi a shekara 1994. Inda ya mikawa Buhari shugabancin hukumar PTF ta yi rawar gani a kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya, PTF ta kyautata bangarori da dama a Nijeriya wadanda suka hada da makarantu, kiwon lafiya, hanyoyi da sauransu. Wanda ‘yan Nijeriya ba za su manta da ita ba.
Bayan mutuwar Abacha a shekara 1998 da kuma dawowar Demokradiyya a shekara 1999, Buhari ya shiga harkokin siyasa da kuma neman takarar shugabancin kasar a shekaru 2003, 2007, 20011, amma ba tare da samun nasara ba, sai a karo na hudu wato a shekara ta 2015 da ta gabata.
Idan muka dubi halin da kasar take ciki a lokacin da Buhari ya sake dawowa a matsayin shugaban kasa a karo na biyu, za mu ga cewa matsalolin da kasar take fama da su sun ninninka wanda ya tarar a shekara ta 1983. Sai dai a yi masa fatan alheri a cikin gagarumin aikin da ke gabansa. Musamman ma yaki da cin hanci da rashawa da ya zama ruwan dare gama gari a kasarmu Najeriya
Ina fata ‘yan Nijeriya za mu ci gaba da baiwa Shugaban talakawa na jam’iyyar APC wanda shi Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ke jagoranta goyon baya da hadin kai domun Gwamnatin sa ta yi nasara wurin ciyar da kasar Nijeriya gaba.
Fatana da kuma addu’ar mu ga Gwamnatin Baba Buhari shine Allah ya ba shi sa’a da nasarar warware matsalolin Nijeriya a wannan yanayin da ya samu kasarmu a ciki.
Haka kuma muna kara godiya ga Allah da ya yi mana ni’iman zaman lafiya a wannan mulkin. Jama’a mu cigaba da addu’ar fatan alkairi ga wannan bawan Allah.
Allah ya kare mana Shugaba Buhari, Allah ya tsare mana Shugaba Buhari. Allah ya baiwa Shugaba Buhari ikon warware matsalolin Nijeriya. Amin.