Wannan maƙalar na ɗauke da muhimmai daga cikin abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da muke bankwana da shi.
Ƙungiyar ƙwadago ta NLC za ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
‘Yan ƙwadago a Najeriya
Kungiyar kwadago a Najeriya ta NLC ta ce za ta fara yajin aiki na gama-gari daga ranar Laraba, 7 ga watan nan na Yuni sakamakon matakin gwamnati na cire tallafin man fetur.
Shugaban kungiyar Joe Ajaero shi ne ya sanar da haka, bayan wani taron gaggawa da shugabannin kungiyar suka yi ranar Juma’a a Abuja.
Kwamared Ajaero ya ce gwamnati musamman ma kamfanin mai na NNPC na da wa’adin zuwa Laraba ya mayar da farashin man fetur kamar yadda yake a da idan ba haka ba za su shiga yajin aikin sai-abin-da-hali-ya-yi da kuma zanga-zanga a fadin kasar.
A ranar Juma’a ne shugabannin suka kira taron domin tattaunawa da bayyana matakin da za su dauka bayan da sabon shugaban kasar ya furta cewa kasar ta janye tallafin mai.
Wannan sanarwa ta shugaban ta janyo tashin farashin man a sassan kasar, inda aka rinka samun dogayen layukan ababan hawa a gidan mai.
Muhimman alƙawuran da Tinubu ya ɗauka a jawabinsa na ranar rantsuwa
Bola Ahmed Tinubu
Daga Litinin, 29 ga watan Mayu, Najeriya ta yi sabon shugaban ƙasa kuma na 16 a tarihi. Sunansa Bola Ahmed Tinubu.
Hakan ya faru ne sakamakon rantsuwar kama aiki da sabon shugaban na Najeriya ya sha a dandalin taro na ‘Eagle Square’ da ke birnin Abuja a matsayin shugaban Najeriya na 16.
Shugabannin ƙasashen duniya kimanin 24 ne suka halarci bikin, kamar yadda wata majiya ta shaida wa BBC Hausa.
Jawabin da Tinubu ya gabatar cike yake da ƙarfafa gwiwar ƴan Najeriya, da neman haɗin kan ƙasa.
Sai dai wasu daga cikin alƙawuran da ya ɗauka sun shafi sake fasalin matakan da gwamnatin Buhari ta ɗauka a fannin tattalin arziki.
Cikin manyan alƙawuran akwai sake duba maganar sauya fasalin kuɗi, da daidaita darajar naira, da tabbatar da cire tallafin man fetur, da samar da aikin yi miliyan ɗaya a ɓangaren fasahar zamani.
Haka nan, an rantsar da gwamnoni 28 cikin 35 a faɗin Najeriya, waɗanda suka yi nasara a zaɓen watan Maris da ya gabata.
Tinubu ya naɗa Femi Gbajabiamila Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa
Asalin hoton, @DOlusegun
Tinubu da Gbajabiamila
Shugaba Bola Tinubu ya nada Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa (Chief of Staff).
Kazalika, an nada Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, a matsayin mataimakinsa.
Sanarwar da ta fito daga darektan yada labarai na fadar shugaban kasar, Abiodun Oladunjoye, ranar Juma’a ta kuma ce Tinubun ya nada tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon ministan ayyuka na musamman na gwamnatin Buhari, Sanata George Akume, a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Takardar ta ce shugaban ya yi wadannan nade-nade ne a yayin taro da gwamnonin jam’iyyarsa ta APC.
Wasu maniyyatan Jigawa sun tsallake rijiya da baya bayan sa’a biyar a sama
Asalin hoton, Hajj Commission
Maniyyata aikin Hajji
Wani jirgin kamfanin Max Air dauke da maniyyata da ya tashi daga filin jirgin sama na birnin Dutsen jihar Jigawa a ranar Laraba ya yi saukar gaggawa a filin jirgi na Mallam Aminu Kano da ke birnin Kano bayan tafiyar wajen sa’a biyar a sama.
Wani daga cikin maniyyatan da ke cikin jirgin da aka samu matsalar ya shaida wa BBC cewa suna cikin tafiya ne sai suka shiga gargada cikin gajimare, daga nan sai aka sanar da su cewa za su koma saboda wata matsala domin a sauya musu wani jirgin.
Ya ce: ”Bayan mun koma mun sauka a Kano sai aka ce mana nan da awa daya za a kawo wani jirgin. To cikin ikon Allah kafin awa dayan ma sai ga aka kira mu muka je muka shiga wanda aka kawo,”
”To kuma muna cikin tafiya mun yi wajen awa biyar da tashi sai aka yi wata sanarwa cewa za mu sake komawa Kano, wasu ma ba su ji sanarwar ba sosai saboda an ce tafiyar wajen awa shida ce kuma mun yi wajen awa biyar, wasu na cewa Jeddah aka ce,” in ji shi.
Maniyyacin ya kara da cewa, ” To muna haka kawai da jirgin ya fara yin kasa-kasa sai muka ga ai nan Kano ne muka dawo.”
Mutumin ya ce daga baya suke jin cewa wai jirgin na biyu ya komo ne saboda wata matsala ta diflomasiyya, ko da yake ya ce ba wata sanarwa ba ce ta musamman illa dai wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin jirgin saman ne da ke tare da su a jirgin suke gaya musu.
Abba Gida-Gida ya fara ɗaukar matakan binciken gwamnatin Ganduje
Asalin hoton, Kano State Governement
Abba Kabir Yusuf
Sabon gwamnan jihar Kano Injiniya, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, ya fara daukar matakan binciken tsohuwar gwamnatin da ya gada ta Abdullahi Umar Ganduje, inda hawansa mulki ke da wuya ya bayar da umarni kan wasu tsauraran matakai.
Daga cikin matakan da ya fara dauka gwamnan ya soke dukkanin cinikin da aka yi na sayar da wasu wurare na gwamnatin jihar.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a jawabinsa na bayan rantsuwa gwamnan ya bayar da umarni ga hukumomin tsaro a jihar su je su karbe iko da wadannan wurare da gwamnatin Ganduje ta sayar.
Wasu daga cikin wuraren da aka sayar sun hada da filayen makarantu da na masallatai da makabarta da jikin badala da sauransu.
Matakin bai tsaya ga kadarorin gwamnati da ke cikin jihar ba har ma da wadanda suke waje dokar soke cinikin ta shafesu.
A daina fargaba muna da wadataccen mai — NNPC
Yayin da aka fara dogayen layuka a gidajen mai a wasu sassa na Najeriya bayan sanarwar cire tallafin mai da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya ce zai yi, kamfanin mai na NNPC, ya ce jama’a su daina fargaba domin akwai wadataccen mai a kasa.
Shugaban kamfanin, Malam Mele Kyari, ya shaida wa BBC cewa, akwai mai don haka babu wata matsala da ya ke gani za a iya fuskanta data shafi karancin mai.
“Dama duk lokacin da aka samu irin wannan jawabi daga shugabanni, sai mutane su yi ta tururuwa suna zuwa gidajen mai suna siyan mai fiye da wanda suke bukata saboda suna tsoro kada a kara kudin man” a cewar Kyari.
Ya kara da cewa bai ga abin tsoro ba domin akwai mai sosai a kasa.
Dangane da batun cire tallafin man kuwa, shugaban na NNPC, ya ce dama tallafin ya jima da zame wa NNPC matsala, domin kudin kamfanin ake dauka ana biyan tallafin.
Ya ce: “Abin da shugaban kasar ya yi ya zo dai-dai da dokar kasa, domin matakin hakan ya dace sosai”.
Shi ma shugaban hukumar da ke kula da tsare-tsare da sa ido a kan harkokin man fetur a Najeriyar NMDPRA Malam Faruk Ahmed, ya ce za su tabbatar farashin man bai wuce kima ba.