Kamar kowane mako, mun duba muku muhimmai daga abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata.
An yi zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokokin jihohi
Asalin hoton, INEC
A makon da ya gabata – ranar 18 ga watan Maris aka yi zaɓen gwamnoni da ƴan majalisar dokoki na jihohi a jiha 28 na Najeriya.
Zaben ya yi zafi a wasu jihohin ƙasar da har ta kai ga samun taƙaddama kafin a sanar da sakamakon zabensu.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta bayyana cewa bayan zaɓen, Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar ta ta lashe jihohi 15, sai PDP da ta samu jihohi 9, NNPP da Labour kuma suka samu jiha ɗaya kowannensu.
Akwai kuma jihohi biyu – Adamawa da Kebbi da INEC ta ce zaɓensu bai kammala ba saboda matsaloli da kuma ƙalubalantar zaɓukan da jam’iyyu suka yi kuma zuwa yanzu hukumar ba ta ayyana ranar da za a sake gudanar da zaɓe a jihohin ba.
Zaɓen dai ya samar da zaɓaɓɓun gwamnoni 17 da za su soma mulki da zarar an rantsar da su a watan Mayu.
Akwai kuma gwamnoni masu ci guda tara da aka sake zaɓa domin yin wa’adi na biyu.
Zaɓen ya bar waɗansu ƴan siyasa cike da murna yayin da wadansu ƴan siyasar suke cike da bakin ciki, saboda yadda sakamakon ya kasance.
A waɗansu jihohin ƙasar an samu sauyi a jam’iyyar da ke mulki inda ƴan adawa suka samu nasara a yayin da a waɗansu kuma masu mulkin ne suka samu dama domin ci gaba da jan ragama.
Musulmi sun soma ibadar azumi
Asalin hoton, Getty Images
Mai alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya sanar da ganin jaririn watan Ramadan na shekarar 2023 a wasu sassan Najeriya.
A jawabin da ya yi na sanarwar wanda aka sanya a shafin Tuwita na kwamitin ganin watan, Sarkin Musulmin ya ce an ga watan ne bayan samun rahotanni daga shugabannin addinin Musulunci da ke wasu jihohin ƙasar.
A ranar Alhamis 23 ga watan Maris din 2023 ne al’ummar Musulmi a Najeriya suka tashi da azumin.
Musulmi fiye da miliyan dubu ɗaya ne suka fara ibadar azumi a faɗin duniya inda za su shafe tsawon wata guda suna azumin na watan Ramadana.
Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam
Asalin hoton, FACEBOOK/EKWEREMADU
Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam.
Shari’ar ta shafi ɗauko wani ɗan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa ɗiyar Ekweremadun.
Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa ƙoda.
Masu shigar da ƙara sun ce za a cire ƙodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25.
Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata.
Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas.
An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke birnin London.
Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya.
Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da gudumawar ƙoda, to amma hakan kan zama laifi idan har za a biya wanda zai bayar da ƙodar.
A lokacin da aka gane cewar ba za a iya amfani da ƙodar mutumin ba, kotun ta gano cewa iyalan na Ekweremadu sun mayar da hakalinsu wurin samun wani mutumin na daban a ƙasar Turkiyya.
Sai iyalan na Ekweramadu waɗanda ke da gida a birnin London sun musanta tuhumar da aka yi masu.
Ƙarancin Naira: CBN ya umarci bankuna su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi
Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan ƙasar da su yi aiki ranar Asabar da kuma Lahadi domin tabbatar da cewa takardun kuɗaɗen naira sun wadata a hannun jama’a.
A wata sanarwa da CBN ya wallafa a shafin Tuwita, ya ce ya fito da maƙudan takardun naira ne a bankunan ƙasar da kuma na’urorin cirar kudi ta ATM domin magance matsalar ƙarancin kuɗin da ake fama da ita a fadin ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa CBN ya bayar da umarnin ɗaukar takardun kuɗaden daga rassansa zuwa bankunan kasuwanci da ke fadin ƙasar
Ta ƙara da cewa bankunan kasuwancin ƙasar sun samu maƙudan takardun kuɗaɗe domin rarraba wa abokan huldarsu, da nufin wadatar kuɗade a hannun jama’a.
Sanarwar ta ci gaba da cewa babban bankin ƙasar ya umarci bankunan kasuwanci da su sanya takardun kuɗaden cikin na’urorin cirar kudinsu na ATM, domin sauƙaƙa wa kwastomominsu.
Kotu ta tabbatar wa Adeleke na PDP nasarar gwamnan Osun
Kotun daukaka kara a Najeriya ta tabbatar da Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar Osun na ranar 16 ga watan Yuli 2022.
Da wannan hukuncin kotun wadda ta zauna a Abuja ta soke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta jihar ta yi, wadda ta zartar da cewa ba shi ne ya yi nasara ba, abokin hamayyarsa na APC Gboyega Oyetola ne ya ci zaben.
A hukuncin da kotun ta farko ta yi, ta zartar da cewa dan takarar na PDP ba shi ne ya samu mafi rinjayen kuri’u ba, saboda haka ta umarci hukumar zabe ta karbe takardar shedar zaben da ta bai wa Adeleke, ta mika wa Oyetola.
To sai dai a wannan hukuncin na kotun daukaka karar, wanda alkalan kotun uku bisa jagorancin mai shari’a Mohammaed Shu’aibu duka bakinsu ya zo daya, ta soke wancan hukuncin kotun sauraron kararrakin gwamnan, inda ta ce
Adeleke shi ne halastaccen gwamnan jihar ta Osun.
Musanta ganawar Tinubu da alƙalin alƙalai a London
Zaɓabben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya musanta rahotannin da ke cewa ya gana da babban jojin Najeriya a birnin London na ƙasar Ingila.
Wata sanarwa da ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga, ta bayyana labarin a matsayin ƙage maras tushe.
A cikin kwanakin nan ne wasu jaridu da kuma masu amfani da shafukan sada zumunta suka rinka yaɗa labarin yadda aka yi wata ganawar sirri, tsakanin Bola Ahmed Tinubu da babban jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola.
Labarin ya nuna cewa babban jojin ya yi ɓadda-bami ta hanyar hawa keken guragu domin ganawa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a birnin London.
Sai dai sanarwar, wadda aka fitar ta ce an ƙirƙiri labarin ne domin sanya shakku a zukatan ƴan Najeriya game da nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen da ya gabata.
Sanarwar ta ce “muna musanta wannan labari na ganawa tsakanin zaɓabben shugaban ƙasa da babban jojin Najeriaya, da ƙaƙƙarfar murya.”
A cikin sanarwar, Mr Onanuga ya ce yanzu haka Bola Tinubu, wanda ya bar Najeriya a ranar Talatar da ta gabata , yana a ƙasar Faransa, inda yake hutawa domin sauke gajiyar yaƙin neman zaɓe.
Sai dai ya ce Tinubun zai isa birnin London ne nan gaba, kafin ya tafi Saudiyya domin yin Umara.
A cikin watan Fabarairu ne Tinubu ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya inda ya samu galaba a kan Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour.