Wanda ya kai hari a Jamus na dauke da tutar IS a …


 

Hukumomin Jamus sun bayyana cewa, an samu tutar kungiyar IS a dakin matashin da ya kai harin adda da wuka kan fasinjojin jirgin kasa a yammacin jiya litinin a kasar.

Matashin mai shekaru 17 kuma dan asalin kasar Afghanistan da ke gudun hijira a Jamus ya raunana mutane hudu a harin wanda ya kai a birnin Wurzburg na Bavaria.

Sai dai Ministan cikin gidan Bavaria Joachim Herrmann ya ce, ya yi wuri su iya ganowa ko matashin dan kungiyar IS ne ko kuma dai ya dauki irin akidarsu ce a ‘yan kwanakin nan.

Tuni dai jami’an ‘yan sanda suka harbe shi har lahira a lokacin da yake kokarin guduwa daga inda ya aikta ta’asar.

Rahotanni sun ce, an ji maharin na cewa, Allahu Akbar, wato Allah mai girma a yayin kaddamar da farmakin.

Harin na zuwa ne bayan wanda wani matashi ya kai birnin Nice na Faransa inda ya hallaka mutane kimanin 84 da ke bikin ranar samun ‘yan kan kasar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like