Sulaiman Hashimu wanda ya yi tattaki daga jihar Lagos zuwa Abuja domin taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar cin zaben 2015, ya sha alwashin kewaye jihohin Nijeriya guda 36 ciki har da Abuja.
Sulaiman wanda ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na NAN hakan a yau Juma’a, ya ce a wannan karon ba tattaki zai yi da kafa ba a mota zai zagaya, kuma zai yi hakan ne domin ya ganewa idonsa abubawan da gwamnatin Buhari ta yi a johohin kasar nan.