
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren kwadago na Amurka Marty Walsh ne zai zama jami’in da zaa keɓe a bana
Duk lokacin da Shugaban Amurka ya je majalisar ƙasar domin gabatar da jawabin da ya saba yi wa Amurkawa a kowace shekara, za ka ga waɗanda ake kira “wane da wane” na duka manyan birnin Washington da suka haɗa da ‘yan majalisa da manyan alƙalai da manyan dakarun soji, duk suna zaune a gefen shugaban ƙasar.
Amma a do wanne lokaci za a ga babu wani mutum giuda, wanda ake kira “keɓaɓɓen magaji” mutumin da ake boyewa saboda ko ta kwana, ko da suka waɗannan manyan mutane za su mutu to akwai wanda zai iya ci gaba da gudanar da gwamnati.
A wannan shekarar Ministan kwadago Marty Walsh shi ne keɓaɓɓen magajin. A bara kuma ministan kasuwanci Gina Raimondo aka keɓe.
A cewar wata cibiya a Amurka an fara wannan al’ada ne a shekarun 1950, lokacin da aka fara barazanar yaƙin nukiliya tsakanin Amurka da tarayyar Soviet wanda ya ƙare a yaƙin cacar baka.
A 1981 ne gwamnatin Amurka ta wancan lokaci, ta fara bayyana mutumin da aka keɓe. A shekarar Terrel Bell ne aka ware wanda shi ne ministan Ilimi na ƙasar.
Tun daga nan aka koma ɗaukar wannan keɓaɓɓen mutum daga cikin masu riƙe da gwamnati ko hukumominsu, abin ya haɗa da ministan shari’a da kuma wasu jami’ai masu riƙe da manyan muƙamai.
jami’an da aka tsaba ga wannan matakin a baya
A lokacin Shugaba Donald Trump, majalisa Amurka ta keɓe ministocin noma da makamashi da kuma na cikin gida.
Shi wanda ake keɓewa ya zama magajin dole ya kasance yana da ikon da fadar shugaban ƙasa za ta iya ayyana shi a matsayin, kuma zai riƙe matsayin shugaban sojin ƙasar ne kawai idan duka masu babban matsayin da za su iya rike wajen ba za su iya ba.
Cikin abubuwan da za su bayar da dama ga wanda zai yi gadon, dole ya zama mutumin da aka haifa a Amurka, ma’ana wanda ya samu shaidar zama ɗan ƙasa kamar ministan tsaro Alejandro Mayorkas da na makamashi Jennifer Granholm ba za su taɓa riƙe wannan matsayi ba.
Da wannan matsayi ba shi da wani mahimmanci a cikin al’umma, har sai da Hollywood suka yi wani abu a kansa.
Wani shiri na talabijin wanda jarumi Kiefer Sunderland ya taka rawar ministan gidaje da raya birane ya ɗare gwamnati bayan wani harin bam da ya tashi a majalisa.
Amma a zahiri, matsayin ba shi da wani martaba. A bara, Ms Raimondo ta kalli bayanin ne daga wani keɓaɓɓen wuri, amma bayan haka tana gudanar da rayuwarta ne yadda take yau da kullum.