Wane Ne Sahabin Annabi ( S. A. W) Sayyadina Abubakar? Shine: Abdullahi bn Usman bn Aamir bn Amr bn Ka’ab bn Sa’ad bn Tamim bn Murrah bn Ka’b bn Lu’ai bn Ghalib bn Fihr Alquraishy At taimy. Ana kiran sa da Assiddiq saboda Gasgata Annabi (S.A.W) da yayi lokacin da yai Isra’I da Mi’iraj, Ana kiran sa Atiq Ma’ana wanda Allah ya kubutar daga wuta.
Shine Mutum na farko da ya fara karbar musulunci, Shine Babban Sahabi, Abokin Annabi (S.A.W), Shine Surikin Annabi, Shine wanda Annabi ya fiso a duk duniya, Shine wanda ya bayar da dukiyar sa saboda Allah, Shine wanda yayi hijira tare da Annabi, Shine wanda ya sayi filin da aka gina Massalacin Annabi a Madina, Shine wanda Annabi yace a rufe kowacce kofa ta shiga Masallaci amma a abar ta Abubakar, Shine wanda Matar sa ta ki Musulunta ya sake ta, Shine wanda Mutane da yawa suka shiga musulunci ta sanadin sa. Ga kadan daga cikin su:

-Usman bn Affan

-Al-zubair

-Dalha ibn Ubaidullah

-Abdulrahman bn Auf

-Sa’ad bn Abi Waqqas d.s
Haka kuma Shine wanda ya yantar da bayi saboda musulunci kamar su:

-Bilal ibn Rabi’ah

-Abu Fakih

-Ammar Ibn Yasir

-Lubaynah

-Umm Ubays
Shine Wanda Ya halacci yakoki da dama tare da Annabi don daukaka kalmar Allah, Shine wanda Annabi ya Halifantar da shi tun yana da rai…..Kai Shine! Shine!! Shine!!! Wanda Allah ya yarda da shi, ya bashi Aljannah tun yana raye..
Kai madalla da Assiddik abun alfahari, abin takama, abin koyi, Shugaba Nagari, Zababbe daga Allah da Manzon Allah, Mai Daraja ta uku a Duniya in ka dauke Annabawa.
Wannan kadan kenan daga darajar Sayyadina Abubakar, Sanin Hakikanin waye Sayyadina Abubakkar wannan sai Allah.

You may also like