Wani bam ya fashe a Spain


 

 

 

Wani bam ya fashe a  wani gidan shan kofi na birnin Velez-Malaga da ke kasar  Spain,inda ya yi sanadiyyar jikkatar mutane 77.

5 daya cikin wadanda suka raunana na cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Bayan wannan mummunan lamarin wanda kawo yanzu ba’a tantance dalilin faruwarsa, an isa da wadadan suka jikkata zuwa asibiti a cikin motocin ‘yan sandan yankin.

Ana kyautata zaton wannan lamarin da da alaka da ta’addanci.

You may also like