Wani Barawon Mutane Yayi Amfani Da Kudin Fansa Wajen Bude Shagon Siyarda Kayan Masarufi


 


Jami’an tsaro sun kama wani Umar Abubakar, wanda suke zargi da kasancewa daya daga cikin wadanda suka sace matar gwamnan babban bankin Nijeriya Margret Emefiele a watan Satumbar bana.

Rahotanni na nuna cewa Abubakar ya yi amfani da kason sa na kudin fansan da suka karba wajen bude makeken shagon sayarda kayan masarufi, wanda shi da matarsa ke kula da.

Jami’an tsaron sun ce Abubakar ya yi amfani da kimanin Naira Miliyan 3 a cikin kudin fansan na sa wajen bude shagon.

Haka kuma ya sayi gidaje biyu da filaye guda uku.

Wata sanarwa da jami’an tsaron suka fitar ta bayyana cewa an kama Abubakar ne a garin Minna da ke jahar Niger a ranar 9 ga watan Disambar nan.

Sun ce tuni sun samu nasarar karbo takardun gidajen da filayen, kuma sun kulle shagon

You may also like