Wani  Barawon Ragon Sallah  Zai Shafe Watanni 6 A Gidan Yari  


Yayin da iyalan ke fafutukar abinda za su yanka a ranar Sallah.

Shi kuwa wani mutum dan shekara 30  mai suna Suleiman Awokunle, a jihar Osun  hukuncin daurin watanni shida aka yanke masa a gidan  yari kan laifin satar ragon Sallah.

Yan sanda sun shaidawa kotu cewa darajar ragon takai N25000.

Mai laifin yaki yarda da aikata laifin da ake tuhumarsa dashi kana ya roki alkali kan yayi masa sassauci.

Alkalin kotun yayi masa sassauci inda ya bashi zabin biyan tarar N4000 saboda yanayin bikin Sallah da ake ciki. 

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like