Wani Bom Ya Tashi A Birnin Maiduguri Na Jihar Borno Ya Kuma Kashe Mutane Biyu


 

Majiyar jami’an yansanda a birnin Maiduguri babbin birnin Jihar Borno a arewa maso gabacin tarayyar Nigeria ta bayyana cewa an kai hari da bom a wata unguwa a birnin a safiyar yau Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto kakakin rundunar  yansanda a jihar Mr Victor Isaku yana fadar haka ya kuma kara da cewa harin ya auku ne Garejin Muna kan hanyar Baga da misalin kar 9 na dare sannan dan kunan bakin waken da wani mutum guda ne suka rasa rayukansu a harin. Sai kuma wata motar marcides da ke tsaye a kusa da wurin ta lalace.

Mr Isaku ya kara da cewa a ranar Jumma’an da ta gabata ma, wani dan kunan bakin wake ya tada bom a garejin na Muna amma ya kashe kansa shi kadai ne. Har’ila yau wani dan kunan bakin waken ya yi kokarin shiga sananin yan gudun hijira kusa sa rukunin gidaje na Custom amma jami’an tsaro sun kashe shi kafin ya kai ga sansanin. Sannan a lokaci guda wani dan kunan bakin wake, a dai dai lokacin ya kashe kansa a kan hanyar Gambaru Ngala.

You may also like