Wani Dan Achaɓa Ya Kashe Kansa Ta Hanyar Rataya 



Wani mutum mai suna Shehu Abdul ya halaka kansa ta hanyar rataya a unguwar Kaduna Efekpe dake garin Anyingba a karamar hukumar Dekina a jihar Kogi. 

Lamarin wanda ya auku a ranar Talatar da ta gabata, wani dan uwan mamacin mai suna Hamza Abdul ya bayyana cewa, marigayin wanda yake aikin acaba a garin na Anyingba, ya jima yana barazanar kashe kansa saboda kuncin rayuwa da ya tsinci kansa a ciki. Inda a koda yaushe ‘yan uwansa suke lallashinsa.

You may also like