Wani dan daba ya kai hari a jam’iar Ohio ta Amurka inda ya cakawa mutane 11 wuka tare da jikkata su.
Maharin ya shiga makarantar da motarsa inda ya fito tare da cakawa mutanen da ke kusa da shi wukar da ke hannunsa.
An bayyana cewa, maharin wani dan kasar Somaliya ne mai shekaru 18 mai suna Abdurrazak Ali Artan.
‘Yan sanda sun harbe maharin tare da kashe shi.
Ana bincike kan ko harin na da alaka da ta’addanci ko kuwa a a.