Wani Dan Kabilar Igbo Dake Kano Ya Dinkawa Almajirai Kayan Sallah  


Almajiran Lokacin da suke bin layi domin tela ya dauki gwajinsu

Hausawa suka ce “Ba duka aka taru aka zama daya ba,” tabbas malam Bahaushe yayi gaskiya a wannan magana tashi, yayin da wasu yan kabilar Igbo karkashin jagorancin Nmandi Kanu,  suka dukufa wajen ganin cewa kasarnan ta wargaje.
A  gefe guda kuma wasu yan kabilar Igbo sun dukufa wajen ganin dorewar kasarnan kasa guda. 

Ba komai ne yasa nace haka ba sai ganin yadda rahotanni ke cewa wani dan kabilar Igbo dake zaune a kasuwar Sabon  Gari dake Kano ya tara Almajirai har guda 30 domin yi musu dinkin sallah.  

Jama’a da dama a shafukan sada zumunta sun yaba da irin wannan kokari da  mutumin yayi inda suka ce hakan zai kawo hadin kan kasa, musamman a wannan lokacin da ake musayar zafafan kalamai tsakanin kungiyoyi da suka fito daga yankin kudu maso gabas da kuma wadanda suka fito daga yankin Arewa. 

You may also like