Wani Dan Kasuwa A Jihar Yobe Ya Aurar Da Mata Marayu Da Nakasassu Guda 50Wani Shahararren Dan Kasuwa A Jihar Yobe Mai Suna Alh. Mohammed Yakubu Jacob Ya Aurar Da ‘Yan Mata Marayu Da Marasa Galihu Akalla Su 50 A Kofar Fadar Mai Martaba Sarkin Bade Alhaji Abubakar Umar Sulaiman.
Wannan Al’ amarin ya dauki Hankalin Al’umma da dama Kasantuwar Cewa A Cikin Watan Da ya Gabata ma Wannan Bawan Allah Ya Aurar Da ‘Yan Mata 40 A Garin, Bayan Iyaye Da Wasu Wakilai Sun Mika Kokensu A Gare shi.
A cewar Mai Martaba Sarkin Bade, Akasarin ‘Yan Matan Marayu ne Da ‘Yan Gudun Hijira Wadanda Suka Sami Mazajen Aure, Amma Iyayen su Ko Wakilan su Ba su da Halin Aurar Da su Sakamakon Halin Rashi.
A Yanzu Haka dai Wannan Bawan Allah Ya Koyar Da ‘Yan Matan Sana’o’i Daban-Daban Tare Da Basu Jari Domin Dogaro Da Kai, Sannan Fadar Sarkin Ta nada Wani Kwamiti Da Zai dinga yin Sulhu A Tsakanin Ma’auratan Dan Samun Kyakkyawar Fahimta A Cikin Rayuwarsu Ta Aure.

You may also like